A yayin da al’ummar musulman duniya suka fara azumin watan Ramadan na wannan shekara, muna kira ga masu hannu da shuni dama shugabannin al’umma da su taimakawa masu dan karamin hali da abin da zasu rinka yin sahur da kuma buda baki da shi, musamman a jahar mu ta Zamfara da rikici ya raba dubban mutane da muhallansu, domin kowa ya taimaki wani to Allah zai taimake shi.
Daga Mahmud Salihu Kaura Namoda, Zamfara, 09079551996.
Ramadan: Kira ga malamai
masu tafsir
Malamai da ke gudanar da Tafsiri a cikin watan Azumin Ramadan. Da fatan zaku rinka gudanar dashi kamar yadda alkur’ani ya tsara, domin jama’a su amfana. Banda yin habaici ko Shagube ko Gugar zana ko Yarfe da Kazafi ga wadanda ba akidar ku daya dasu ba. Da fatan za a fara a kuma kammala lafiya.
Daga. Madugun Kungiyar MURYAR JAMA’A. Katsina.07039205659
A saki Abu Ammar a tunkari
sauran matsaloli
Salam Edita, ka bani dama na yi tambaya ga gwamnatin jihar Katsina mene ne laifin (Malan Abu Ammar) ko gwamnati na nufin karya Malan ya fada? Mu jama‘ar karamar hukumar Danmusa mune zamu bada labarin abubuwan da ke faruwa musamman a kauyukan karamar hukumar. Don haka yakamata a saki malan a tunkari matsalolin da muke fuskanta tsakani da Allah musamman a wannan lokaci na saukar damina.
Daga Kabir Yunusa Abdussalam 08062627138
A hukunta wadanda suka
yi wa Zainab sharri
Assalam Aminiya, zan yi tsokaci game da wadanda suka yi wa Zainab Aliyu sharri game da kwayoyi masu bugarwa, bai kamata a barsu ba, yakamata a kaisu gidan yari ya zama reshe ya juye da mujiya wasalam.
Daga Lawan Diraiban Tanki Rapin jaki Jos ta Arewa 08121767177.
Matsalar ruwan sha: Jama’ar Shanono na yin hijira
Assalam Edita, muna rokon Gwamnatin jihar Kano don Allah ta taimakawa jama’ar garin Shanono da ruwan famfo daga Bagwai domin a yanzu mutanen da suka tashi suka koma jihar Katsina suna da yawa. A yanzu muna sayen jarka Naira 70 dan haka, wadanda muka zaba tunda sunki yin komai, su sani cewa, (Karshen Dan farauta Kidan Garaya).
Daga Tukur Maraya Shanono, 07032442923.
Ramadan: A tausayawa mabukata
Salam, Aminiya, mafi daukakar jaridar Hausa. Don Allah ku mika min kira na ga ‘yan uwa musulmai da mu tausayawa juna ta hanyar ciyar da mabukata a cikin watan azumin Ramadan.
Daga Hafsat Usman, Kuwait Kano 07030020056.
Kira ga Gwamnatin Jihar Bauchi
Assalamu-alaiku Edita. Dan Allah ka bani dama in yi kira ga gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Barista M. A. Abubakar. Da ta kawo mana agajin gaggawa na rashin ruwan sha domin a gaskiya matsalar ruwan sha a cikin garin Bauchi yana nema ya gagari kundila ganin yadda al’umma ke shan bakar wahala wajen nemo ruwan da zasu sha ina kira da babbar murya ga masu ruwa da tsaki kan wannan lamari da su yi duk mai yuwuwa wajen ganin sun kawo karshen wannan matsala na rashin ruwa. A karshe nake addu’ar Allah Ya sa wannan kira nawa ya kai ga inda ya dace Ameen summa Ameen.
Daga Sani Mohammed Chindo. Unguwar karofin madaki a Bauchi 08030918913.
Talakawa na neman agaji
Ka taimakawa talakawan ka, da ka share musu kukansu da a daina kashe su a wasu yankuna.
Daga Shuaibu Abdullrrahman Kawo Lambu Nassarawa Kano, 07065143333 .
Sakon taya murna ga kasuwar
Mile 12 Legas
Salam Editan Aminiya mai albarka da fatan kuna lafiya amin. Ina so ka taimake ni da wannan fili namu na mika sakon taya murna ga sabon shugaban kasuwar Mile 12 Legas Alhaji Shehu Samfam da Sakataren Alhaji Uban Bala da sauran su da fatan Allah ya taimake su riko amin.
Daga Alhaji Jinjiri na Alhaji Shaaibu Mile 12 Legas 09023489162.
Gwamnan Bauchi ka
rungumi kaddara
Assalam Edita, ina so ka bani dama in yi kira ga gwamnan jihar Bauchi mai barin gado ya yi hakuri ya rungumi kaddara mulki nufin Allah shi yake bayarwa shi yake hanawa.
Daga Nasir Malami Sidi Bauchi, 08036311157.
Kira ga Gwamnati a dauki
matasa aikin aikin yi
Salam Edita, dan Allah ka bani dama na baiwa Baba Buhari shawara akan matsalar tsaro a Najeriya a ganina daukar matasa aikin soja da dan sanda da sauran aikin damara dan inganta tsaro a kasar nan duba da yadda matasa suke san aikin har kudi suke kashe wa domin nasan mutane da yawa da suka kashe kimanin Naira dubu 150 amma a banza, kamar bayan kasa ba kuma gashi ana cewa jami‘an tsaron ba sufi mutum miliyan 10 ba ma a kasar a ganina baiwa matasa aiki shi ne kawai mafita a kasar nan ya Allah Ka zaunar mana da kasarmu lafiya.
Daga Baban Abbas Kano, 09033168513.
Gaskiya ta yi halinta
A daina ganin laifin Baba Buhari. Matsalolin da ke faruwa a Arewa sun yi yawa. Kisa, sata da yin garkuwa da mutane ya kamata gaskiya shugabannin tsaron Najeriya su aje aikin su. Sai a canza wasu, tunda na yanzu sun kasa tabuka komai. Banga dalilin da zaisa ace: Ministan Shari‘a, tsaro, da cikin gida Shugabanni irin:- ‘yan sanda, Kwastam, Jami’an tsaron shige da fice, jami’an tsaron DSS, Sojoji, sojojin sama da sauran manyan jami’an tsaro duk ‘Yan Arewa ne, mene ne amfaninsu. Ana ta yi wa Arewacin Najeriya hawan karen tsaye. Sun kasa yin komai. Sai su sauka tunda sun gaza. Suke wakiltar Baba.
Daga Yusuf Isah C. Kangiwa, 08029815330
Kira ga Buhari game da zaben Kano
Assalam Jaridar Aminiya, dan Allah ku mika min sakona ga shugaba Muhammadu Buhari ya sa baki akan zaben Kano duk wanda yaci a ba shi.
Daga Mustafah Mai Taki Fulatan Rogo Jihar Kano, 09073888085.
Kira ga Shugaba Buhari
Zuwa ga Muhammdu Buhari da fatan zaka rika duba halin da talakawa suke a halin yanzu ka duba ka gani.
Daga Aminu Askoza 08065416485.
Ramadan: Masu hali ku taimaka
wa mabukata
Kyautatawa nasa soyayya a zukatan juna. Don Allah masu hali ku taimakama mabukata a wannan watan ramadan.
Daga A. S. Gwani Zariya (izala boy), 07068274370.
Shugabanni akwai mutuwa da hisabi
A gayama masu madafan iko idan akwai karewar wa’adin mulki to akwai mutuwa ta na biye akwai kuma hisabi ga kowa da kowa. Allah Ya cece mu tare da rahamarsa da jinkansa, amin.
Daga 08135419744.
‘Yan sanda a duba masu boye lamba
Aminiya ku bani dama domin ba shugaban ‘yan sandan Najeriya shawara da ya yi binciken duba yadda masu motocin kansu ke boye lambar motarsu (plate number), domin inganta tsaron kasa.
Daga M.Aliyu Gambo. 08027878754.
Zagayowar wata mai alfarma
Salam, Aminiya ku isar min da sakon taya murnata, dangane da zagayowar wata mai alfarma, ga daukacin musulman duniya, tare da fatan Allah Ya bamu ikon aiwatarwa, ya kuma karba mana amin.
Daga Dahiru Dauda (KGY) Bindawa, 08055552897.
Satar mutane: A binciki PDP
Assalam Edita, ya aiki, Allah Ya kara daukaka jaridar AMINIYA Amin. Yakamata shugaba Buhari ya tsananta bincike akan yawan sace sacen mutane da ake yi musamman akan jam`iyyar adawa ta PDP domin zata iya yin komai saboda taga ta bata mulkin APC saboda zafin shankaye musamman na shugaban kasa zasu iya kashe kowa saboda, saboda gwamnatin Buhari to ta Allah ba taku ba.
Daga Yahaya Ahmed Jabo Apapa Lagos 08128286038.
Sakon barka da azumi ga
jagorori nagari
Salam dan Allah Edita ka bani dama na mika sakon barka da shigowar watan azumin Ramadan ga jagorori masu kaunar talakawansu kamar irin su shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnan Kano Ganduje tare da Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim da sauran jagorori masu kaunar talaka da fatan Allah Ya sa muga karshen watan lafiya.
Daga Shehu M. Sule Getso, 07037079900.
Ba karin masarautu ba ne matsalar talakawan Kano
Salam Aminiya ina son a isar da wannan sakon nawa ga ‘yan majalisunmu na dokoki na jihar Kano, game da neman kirkiro da wasu sababbin masarautu anan jihar Kano da kuka ce wai wasu kungiyoyi sun bukaci ayi, to ni a nawa ganin ba karin masarautu bane matsalar talakawan jihar Kano haka kuma ina ganin zaifi a gudanar da kuri‘ar jin ra‘ayin jama‘ar jihar Kano ba wai ta wasu tsurarin kungiyoyi ba.
Daga Abdullahi Umar (A.U) Kano, 08063511757.