Gwamnatin Jihar Kaduna ta ayyana ranar Laraba, Alhamis da Juma’a a matsayin ranakun hutu domin bai wa ‘yan jihar damar kammala rijistar zabe.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamna Nasir El-Rufai shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya raba wa manema labarai a jihar.
- Yajin aikin ASUU: Kungiyoyi 47 sun shiga zanga-zangar NLC a Kaduna
- Matsalar tsaro: NNPP ta bukaci Buhari ya yi murabus
Ya kuma bukaci daukacin al’ummar jihar da su yi rajistar katin zaben don amfani da ‘yancinsu na kada kuri’a.
Ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su yi rijistar zabe kafin ranar 31 ga watan Yuli 2022.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin, ta bukaci dukkan ma’aikata da su tallafa wa ma’aikatansu don yin rajistar katin zaben, kafin INEC ta rufe rajistar a ranar 31 ga watan Yuli, 2022.