✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’

Idan zaɓe na gaba ya zo, babu wanda Hausawa za su sake zaɓa sai ɗan uwansu Bahaushe.

Wata ƙungiya mai rajin kare muradun al’ummar Hausawa a Nijeriya mai suna Kungiyar Hausawan Nijeriya ta tsaya kai da fata cewa dole a ƙyale Hausawa su kafa ƙungiyarsu kamar kowacce ƙabila tun da dai doka ba ta hana su ba.

Martanin nasu na zuwa ne a daidai lokacin da masu kiran ke shan sukar cewa suna ƙoƙarin rura wutar ƙabilanci ne a Arewacin Nijeriya Najeriya, musamman a daidai lokacin da yankin ke buƙatar haɗin kai domin magance matsalolinsa.

To sai dai ƙungiyar ta ce ba ta ga dalilin da zai sa a ƙalubalanci yunƙurin nasu ba, tun da dai ’yan ƙabilar Yarabawa suna da ƙungiyar Afenifere, ’yan kabilar Ibo suna da Ohaneze, Fulani kuma suna da Miyetti-Allah.

Sun ce hakan na nufin Hausawa ne kawai a cikin manyan ƙabilun ƙasar ba su da ƙungiyarsu ta ƙashin kansu.

A yayin wata zantawarsu da manema labarai a Kano, shugaban kungiyar, Abdullahi Abdullahi, ya ce yunƙurin ya zama wajibi domin kare muradun Hausawa a ƙasar ta kowacce fuska, musamman ta ɓangaren tsaro da ya ce ’yan bindiga na neman hana Hausawa rayuwa a yankunansu.

A cewarsa, “Akwai yunkurin da ake yin a kore samuwar asalin Hausawa ta hanyar cewa a yanzu babu cikakkun Hausawa na asali, a daidai lokacin da ake kiran wasu da cikakkun ’yan kabilar Ibo, Yarabawa da Fulani.

“Ayyukan ta’addancin da ake yi wa Hausawa a kasarsu abin takaici ne.

“Ina wadanda suka kashe Sarkin Gobir? Ina mutanen da Bello Turji ya ƙone ƙurmus a motar bas a Sakkwato ranar da Buhari ya tafi Legas ƙaddamar da littafi?

“Ina matan da ’yan ta’adda suka yi wa fyade a masallaci? Ina labarin jariran da ’yan ta’adda suka ba wa karnuka suka cinye da ransu? Ina labarin mafarautan da aka kashe a jihar Edo a kwanan nan? Waye zai nema musu hakki kuma waye zai bi musu kadi?

“Dole wadannan abubuwan suka sa dole mu Hausawa mu tashi tsaye mu tunkare su tare da masu goya musu baya daga cikin malaman addini, ’yan siyasa, masu rike da sarautun gargajiya da dukkan kungiyoyinsu,” in ji shugaban kungiyar.

Kungiyar ta kuma ce sam ba ta goyon bayan kiran da wasu ke yi na a yi wa rikakken dan ta’addan nan, Bello Turji afuwa, inda suka ce hakan babban kuskure ne da za a yi da-na-sani a kai.

Daga nan sai ƙungiyar ta yi Allah-wadai da abin da ta kira rashin sanin ciwon kai, kan yadda ta ce an kafa wani babban allon talla mai dauke da rubutun “Katsina babu korafi” ɗauke da hoton Shugaban Kasa Bola Tinubu yayin ziyarar da ya kai Jihar Katsina a ’yan kwanakin nan, a maimakon a fada masa matsalar da ake ciki ta rashin tsaro.

Sai dai kuma ƙungiyar ta ce idan zaɓe na gaba ya zo, babu wanda Hausawa za su sake zaɓa sai ɗan uwansu Bahaushe.