Hukumar da ke Kula da Kafafen Yada Labarai ta Kasa (NBC) ta sanya wa gidan talabijin na Trust TV tarar Naira miliyan biyar saboda yin rahoton binciken kwakwaf kan ayyukan ’yan bindiga.
Gidan talabijin din dai daya ne daga cikin kafafen yada labarai mallakin kamfanin Media Trust, mamallaka jaridun Daily Trust da Aminiya.
Bugu da kari, matakin na zuwa ne kasa da mako daya bayan Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya yi barazanar cewa Gwamnatin Tarayya za ta hukunta su tare da kafar yada labaran kasar Birtaniya ta BBC, saboda yin rahoton.
Hukumar gidan talabijin din ce ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
Ta ce, “Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ta Kasa (NBC), ta ci tarar gidan talabijin na Trust TV Naira miliyan biyar saboda watsa wani rahoton binciken kwakwaf kan ayyukan ’yan bindiga, wanda tashar ta yi ranar biyar ga watan Maris din 2022.
“NBC, a cikin wasikar da ta aiko wa kamfaninmu ranar uku ga watan Agustan 2022, mai dauke da sa hannun Shugabanta, Balarabe Shehu Illela, ta ce ta ci tarar ce saboda rahoton ya saba wa Kundin Watsa Shirye-shirye na Kasa.
“Yayin da muke ci gaba da nazarin wannan matakin, ya zama wajibi mu yi bayanin cewa a matsayinmu na gidan talabijin, muna fifita bukatun al’umma ne ta hanyar fallasa ayyukan ’yan bindigar da ya addabi miliyoyin ’yan Najeriya.
“Rahoton ya bi diddigin matsalar tsaron ne tun daga tushe, wacce bisa ga dukkan alamu yanzu take kokarin gagarar Kundila.
“Ya bankado yadda batutuwa irinsu rashin adalci, kabilanci da raunin shugabanci suka rura wutar rikicin, sannan ta tattauna da kwararru da ma mahukunta a Najeriya da nufin lalubo bakin zaren, cikinsu har da Minista Lai Mohammed da Sanata Sa’idu Dansadau, wanda ya fito daga Zamfara, jihar da rikicin ya fi kassarawa.
“Sauran wadanda aka tattauna da su a cikin rahoton sun hada da malamai irinsu Farfesa Abubakar Saddique na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da Dokta Murtala Ahmed Rufai na Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sakkwato da dai sauransu.
“Rahoton ya kuma fallasa mawuyacin halin da mutanen da rikicin ya shafa suke ciki,” inji sanarwar.
Kafin rahoton dai, ba kasafai ake jin ainihin abubuwan da ke faruwa a rikicin ba, sai dai rahoton ya shiga har cikin dazuka inda ya ji ta bakin ’yan bindigar da ma dalilan da suka sa su daukar makami.