✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rahma Sadau ta fito a fim din Bollywood

Za ta fito a fim din Khuda Haafiz kashi na biyu tare da tauraron Bollywood, Vidvut Jammwal.

Jarumar fina-fina Kannywood, Rahma Sadau, za ta fito a wani fim din Indiya mai suna Khuda Haafiz kashi na biyu.

Daga cikin jaruman da ke cikin fim din da Rahma Sadau za ta fito har da tauraron fina-finan Indiya, Vidvut Jammwal, wanda ya yi fice, musamman a fina-finan fada a masana’antar indiya ta Bollywood.

A shafinta na Instagram, jarumar ta wallata hotonta da darakta a masana’antar fim din kasar Idniya, Bollywood, Jamil Kabri, tana cewa “Ga mu a Bollywood, muna nan tare da @mevidyutjammwal (Vidyut Jammwal)”.

Vidyut Jammwal shi ne babban jarumi a fim din Khuda Haafiz wanda Rahma Sadau za ta fito a cikin kashi na biyu.

Da haka, Rahma Sadau za ta zama jaruma ta farko daga daukacin masana’antar fim din Najeriya da ta fito da fim din Indiya.

Kanwar jarumar, Zee Sadau ma ta yada hotunan jarumar a Indiya, inda ta ce, “Burinmu na fitowa a fim din Indiya ya cika. ’Yar uwata ba sa’arku ba ce don haka ku rika ba ta girmanta.”

Ko da yake babu tabbacin lokacin da za a fara haska fim din na Khuda Haafi kashi na biyu,  wani fostan fim din da aka gani ya nuna ana haska kashi na daya ne da misalin karfe 7.30 na dare a intanet.

Tun a shekarar 2020 aka fara batun yiwuwar fitowar Rahma Sadau a fina-finan masana’antar Bollywood.

A wancan lokaci, jarumar ta sanya hoton daraktan Bollywood, Faruk Kabir a status dinta na Instagram, inda shi ma ya sanya irin hoton a status dinsa, ya kuma ambaci sunanta.

sai kuma a wannan lokaci da jarumar ta wallafa wadannan hotuna.