Kungiyar kwallon kafa ta Everton da ke buga gasar Firimiyar Ingila, ta dauki Rafael Benitez a matsayin sabon kocinta wanda zai ja ragamar horas da ’yan wasanta a kaka mai zuwa.
Benitez mai shekaru 61 wanda kuma tsohon kocin Liverpool ne ya kulla yarjejeniyar kaka uku da Everton.
- JAMB ta yi martani kan sake gudanar da jarrabawar UTME a bana
- Ya kamata farashin man fetur ya haura N280 —NNPC
Sabon kocin na kasar Sifaniya ya maye gurbin Carlo Ancelotti wanda ya ajiye aiki tun a farkon watan Yuni ya koma Real Madrid, inda shi ma a can ya maye gurbin Zinedine Zidane.
Kungiyar karshe da Benitez ya horar a Firimiyar Ingila ita ce Newcastle United, wadda ya ajiye aikin a Yunin 2019.
Daga nan ne kuma ya koma horar da kungiyar Dalian Professional FC a China kuma suka raba gari a watan Janairu bayan shafe watanni 18 tare.
Everton ta ce Benitez zai soma aikin horar da yan wasanta yayin da za su dawo wasannin sharar fage a ranar 5 ga watan Yuli.