A ranar Litinin da ta gabata ne Shugaban kulob din Napoli da ke Italiya ya bayar da sanarwar daukar Rafa Benitez a matsayon sabon kocin kulob din.
dan kimanin shekara 53 Rafa Benitez ya rike kulob din Chelsea da ke Ingila ne a matsayin na wucin gadi daga watan Janairun wannan shekara zuwa karshen kakar wasa ta bana bayan da kulob din ya kori kocinsa na da Roberto De-Matteo saboda rashin tabuka abin kirki.
Zuwan Benitez kulob din Chelsea ya taimaka musu wajen lashe kofin Europa da kuma zama na uku a jerin kungiyoyin kwallon kafa da suka fafata a gasar rukuni-rukuni na Premier a bana.
Bayan an kammala kakar wasa ta bana a Ingila ne da wasu sassan duniya sai kulob din Napoli ya yanke shawarar dauke Benitez don kada wani kulob ya yi musu shigar sauri.
Tuni kulob din ya fitar da sanarwa a kafar sadarwarsa ta yanar gizo inda ya ce “Muna shaida wa duniya cewa mun kulla yarjejeniya da sabon kocinmu Rafa Benitez daga ranar Litinin da ta gabata a birnin Landan”.
Alamu sun nuna kocin Real Madrid mai barin gado Jose Mourinho ne zai gaji Benitez a kulob din Chelsea nan da karshen mako.
Rafa Bentize ya zama kocin Napoli
A ranar Litinin da ta gabata ne Shugaban kulob din Napoli da ke Italiya ya bayar da sanarwar daukar Rafa Benitez a matsayon sabon kocin…
