Daga Ibrahim Abdu Zango
Na ga abubuwa da yawa a tsawon shekaru da dama a wannan makekekiyar kasa tamu Najeriya.
Gaskiya mutane da yawa suna takaicin cewa Najeriya tana karbar bashi daga bankuna, kususan na kasashen Turai, wato Bankin Duniya da Asusun Bada Lamuni (IMF).
- Jarumar Kannywood, Maryam Waziri, ta amarce da Tijjani Babangida
- Ranar Talata za a bude layukan sadarwa a Zamfara – Gwamna Matawalle
Ni dai na ji cewa tun lokacin da muka samu mulkin kai ake ta so Najeriya ta karbi bashi domin wai ta da kafadar tattalin arzikinta! Mun ji cewa Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato kuma Firimiya Arewa na farko ya ce, “Mun zo Amurka domin gayyatarmu da aka yi, kuma ba mu zo don mu nemi wani taimako ba, koda kuwa a leBe wato wani kankanin zare ke nan.”
Sa Ahmadu Bello (Allah Ya jikansa), yake cewa, “Mu ’ya’ya ne ba za mu taba zama ’yan amshin Shata ba, saboda haka kasarmu Najeriya kasa ce mai zaman kanta kuma za mu ci gaba da kyautata wa al’ummarmu koda kuwa da ba da rayuwarmu ne.”
Wani abin sha’awa Najeriya a lokacin wancan mulki na su Sa Ahmadu Bello ba ta tsaya don karbo bashi daga kowace kasa ko bankunan duniya ba, amma lokacin da za a gina Jami’ar Ahmadu Bello an samu wata kasa a kasashen Larabawa ta taimaka watakila bashi ne babu ruwa, ba kamar na yanzu ba inda ake ba da bashi wanda ruwa yake jefa masu karBa cikin masifa!
Kasashen Larabawa a da lokacin “Arab Bank” suna ba da bashi ba tare da neman ruwa ba.
To gaskiya gwamnatin farar hula ta farko wato 1960 – 1966, ta yi rawar gani, domin ta yi abubuwa da yawa da yau Arewa take mora duk da yake an bar wasu abubuwan sun lalace saboda ’yan bokon yanzu sun take komai domin biya wa Turawan mulkin mallaka bukatunsu, na kada kasar ta ci gaba.
Dubi dai jaridar New Nigerian da Rediyon Najeriya na Kaduna da manya-manyan abubuwan da suka durkushe wanda zamani zai zo ba komai mai amfani da yaran zamani mai zuwa za su mora domin ganin yadda yaran yanzu suke yin wasarere da komai a yanzu.
Manyanmu na Arewa maganarsu da burinsu shi ne tara abin duniya kuma ga komai an samu, amma babu amfani ko kaDan, saboda tarawa kawai suke yi domin ’ya’yansu ba al’umma ba.
To gaskiya wannan duk abubuwa ne da suke faruwa a Arewa. Arewa shiyya ce wacce take cike da miliyoyin al’umma masu yawan gaske, kuma idan ka zuba ido sosai za ka iske cewa yawancin yara matasa sun fi yawa a nan, kuma abin bakin ciki su ne suke sukurkucewa wajen rashin Da’a kuma suke cikin wahalhalu masu yawa.
Kullum muna cikin razani, domin masifun da suke faruwa duk hanya ce ta kawa-zucin sai mun yi kuDi ko ta halin kaka! To, Malam mu dawo yawan cin bashin da Najeriya ke yi a shekarun baya zuwa yanzu, mu dai ba mu sani ba cewa ko lokacin mulkin soja lokacin Janar Yakubu Gowon an karBo bashi wato daga 1967 – 1970 wato lokacin Yakin Basasa. An ce gwamnatin Janar Yakubu Gowon ba ta ciyo bashi ba.
To duk yawanci gwamnatocin Najeriya kususan na soja sun karBi wannan matsanancin bashi, domin an samu gwamnatin da ta karbo bashi na jefa Najeriya cikin kunci wanda dole a rage darajar kuDin Najeriya.
Wannan gwamnatin ita ce ta karBo ta kinkimo wani abu wai shi “SAP” wanda wannan tsari shi ne zai hana gwamnati ba jama’ar kasa tallafi, tun daga ilimi, harkar noma, kai da duk wata harkar arziki.
Dukkansu wannan abu wai shi ta da komadar tattalin arziki ya gota shi kawai cuso shi aka yi domin talauta kasa da ’ya’yanta wadda tun wancan lokaci mun shiga cikin yunwa da dukkan ababen ki cikin da’irar Najeriya kuma ko yadda man fetur da dangoginsa suka ta’azzara wannan ma tun daga cewa an karbo bashi da lamuni ban san komai bashi da lamuni suka bambanta ba.
To gwamnatin wancan lokacin ta yi nata, kuma an ga yadda ta kaya wanda duk da waccan hoBBasa sai da Turawan Amurka suka fatattaki gwamnatin wai ta ki bin tafarkin dimokuradiyya, domin rashin ba Dan lelensu mulki wato wancan mutumin kasar Yarabawa, Allah Ya jikan Musulmi.
To an samu shugaban sojin da ya zo ya ce wai shin nawa ake bin Najeriya ne? Aka ce kaza ne, sai ya cure wuri na gugar wuri ya aika Bankin Duniya wanda daga karshe suka ce ba za su karBa ba, amma suka bar kudaden a wurinsu shi ne suka rika yi wa shi wancan shugaban soji marigayi bi-ta-dakulli har kuwa yanzun nan wanda ’yan Kudu suke ta faman yayatawa, bayan kowa ya san ’yan korensu ne, wannan abu haka yake koda yake dai a nan Arewa an samu masu tsananin son mulki sun shiga sawun ’yan Jari-Hujjar da suke yi wa wannan bawan Allah cara, domin kawai Bata masa suna duk kuwa da cewa abin kirki ya yi wa Najeriya.
An ce wai lokacin Janar Obasanjo an ba Najeriya izinin soke lamuni ko bashi na wai kulob Din Faris (Paris Club) da sauransu, kususan na Ingila, sai mutum ya rasa wai Bankin Duniya da takwaransa na lamuni shin ba waDannan kasashe ne suke juya su ba?
Abin bakanta rai shi ne yadda ake ta ingiza mutane su nemi ilimi, haka wajibi ne, domin Allah Ta’ala Ya umarci Annabin Tsira da cewa Ikra’a.
Sai ga shi masu ilimin a Najeriya sai cusa mu cikin dajin jahilci tsundum! Na san wani farfesa wanda ya yi shahara wurin tattalin arziki, wanda lokacin “SAP” ya caccake ta, amma daga baya aka ce Asusun Lamuni ya dauke shi daya daga masu ba shi shawara a Afirka, wai sai aka wayi gari ya ja ribas cewa wancan bayani da ya yi na sukar “SAP” kuskure ne bayan duk da talaucin da kasa take ciki – har gobe din nan a wannan kasa tamu ta Najeriya!
Kuma kullum za ka ji farfesoshi suna sukar abubuwa ire-iren wadannan amma da an jawo su jiki sai su yi shiru su ma su debi nasu arzikin kasa. Ka san da cewa akwai wani farfesan da ya rike mukamin zama shugaban zabe a cikin wannan kasa kuma an ga makudan kudaden da aka zuba domin zaben kuma ya samu yadda yake so, domin ya shigo gari ganin shi ne yawan shaida abubuwan rayuwa, amma yanzu yana cikin masu tereren bisa yadda ake tafiyar da kasa da raunukan da ke ci gaba wurin tsarin tattalin arzikin wannan kasa: Allah dai Shi ne Gwani kuma bashi kan ciyo shi abu ne na tilas, domin manyan kasashen su ne suke juya akalar duniya idan kuma ka ki sai su sa karnukan farautarsu a cikin kowane gefe na mulki.
Allah Ya tsare, kuma sai mun dawo.
Kwamared Ibrahim Abdu Zango Shugaban Kano Unity Forum, Kano.
08175472298