✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Qatar 2022: Yadda Faransa da Maroko za su barje gumi

Ana sa ran daya daga cikin kasashen za ta kai wasan karshe na Kofin Duniya.

Maroko da Faransa za su fafata a wasan kusa da karshe a Gasar Kofin Duniya, wanda ake sa ran daya daga cikinsu zai kai matakin karshe.

Kasashen biyu za su fafata a daren ranar Laraba da misalin karfe 8 na dare agogon Najeriya, kowannensu ke neman buzun dayan domin kafa tarhiri.

Idan aka yi duba da irin rawar da Faransa ta taka tun fara gasar a da ke gudana a kasar Qatar, a iya cewa ba abun mamaki ba ne don an ganta a wannan mataki duba da irin zaratan ’yan wasa da take da su da kuma yadda take murza leda.

A rukuni Faransa ta lallasa Australia da ci 4 da 1, a casa Denmark da ci 2 da 1, sannan ta yi rashin nasara a wasan karshe na rukuni da ci daya mai ban haushi a hannun Tunusiya.

Faransa ta samu tikitin zuwa zagayen ’yan 16 da maki shida, hakan ya sa ta hadu da kasar Poland, ta yi mata wankan jego da ci 3 da 1.

Daga nan ta samu nasarar zuwa matakin Kwata-Fainal, inda ta hadu da Ingila, inda aka tashi kare jini, biri jini a wansa da ya kayatar matuka.

Faransa da jibin goshi ta yi nasara a kan Ingila da ci 2 da 1, inda dan wasanta Tchoumeni da Giroud suka jefa mata kwallo.

Maroko ta ba da mamaki

A bangaren rawar da Maroko ta taka a gasar kuwa ana ganin lallai kwalliya ta biya kudin sabulu, domin kuwa har yanzu ba a zura kwallo a ragarta ba.

Maroko ta fara wasanta na farko da Croatia, inda suka tashi canjaras babu ci, a wasa na biyu kuwa, ta casa Belgium da ci 2 da babu sannan ta ci Kanada 2 – 1 a wasan karshe.

Da haka Maroko ta kammala wasannin rukuni da maki bakwai, ta tsallaka zuwa Matakin ’Yan 16,  inda ta hadu da kasar Sifaniya.

Maroko da Sifaniya sun tashi ba tare da kowa ya zura kwallo a raga ba, aka tafi bugun fanareti, a nan ne Maroko ta doke Sifaniya da ci 3 da babu, daga nan ta samu tikitin zuwa Matakin Kwata Fainal.

A Kwata Fainal ne Maroko ta kafa wani sabon tarihi, bayan ta doke Portugal da ci daya mai ban haushi.

Da hakan ne Maroko ta zama kasa ta farko daga Afirka da ta taba zuwa Matakin Kusa da Karshe, lamarin da ya sa kasashe da dama daga nahiyar ke goya mata baya.

Wannan tarihi da Maroko ta kafa ya sa masu sharhin kwallon kafa ke ganin cewar ba kanwar lasa ba ce, kuma za ta iya kaiwa ga lashe kofin.

Ita kuwa Faransa tun fil azal tana cikin kasashen da aka yi hasashen za su iya lashe gasar, duba da irin ’yan wasan da ta tara da kuma rawar da ta taka wajen lashe gasar a 2018 a Kasar Rasha, wanda yanzu take neman karewa.

Wadannan kasashe biyu dai za su yi wa juna wanki da dauraya, wanda a cikinsu daa zai je wasan karshe, inda zai hadu da kasar da ta yi nasara a tsakanin Argentina da Croatia.