Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta ce akalla mutum miliyan 17 ne ke rige-rigen sayen tikitin kallon Gasar Cin Kofin Duniya ta 2022 da za a gudanar a kasar Qatar.
Adadin masu rububin sayen tikitin gasar mai taken Qatar 2022 ya ninka tikitin kallon gasar da aka tanadar sau biyar, duk da cewa kudin tikitin na kaiwa har Dala 1,600.
Farashin tikitin gasar Qatar 2022 ya fara ne daga Dala 165 zuwa Dala 1,600 a yayinda farashin kujera mafi arha a wasan karshe ya fara da Dala 600.
Kudin babbar kujera gasar ta bana ya haura na 2018 – wanda aka buga a Rasha, kuma Faransa ta lashe – da kashi 45 cikin 100.
Duk da tsada tikitin da kuma ce-ce-ku-cen da ya dabaibaye gasar da kasar Qatar za ta karbi bakunci, FIFA ta ce, “Masoya kwallon kafa a fadin duniya sun nuna sha’awarsu ta zuwa kallon gasar.”
Ta bayyana cewa daga cikin mutum miliyan 17 da suka nemi tikitin, mutun miliyan 1.8 ne suka nemi sayen tikitin kallon wasan karshe da zai gudana a ranar 18 ga watan Disamba, 2022 a Babban Filin Wasa na Lusai mai daukar mutum 80,000, da ke birnin Doha na kasar Qasar.
An matsa wa FIFA lamba
Duk da cewa akasarin masu neman sayen tikitin ’yan kasar Qatar ne, FIFA ta ce ta fuskanci “matsi” daga masu neman tikitin daga kasashen Ajentina, Brazil, Birtaniya, Amurka, Faransa, Indiya, Meziko, Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ta sanar da haka ne a ranar Talata, bayan rufe karbar bukatun masu neman tikitin kallon gasar da za ta gudana a tsakanin watan Nuwamba zuwa Disamban bana.
Tikiti miliyan 3.3 ne dai FIFA ta tanada domin masu kallon wasannin Gasar Cin Kofin Duniya, wadda ita ce farko da wata kasar Larabawa ke karbar bakunci.
Hukumar kwallon kafar dai na sa ran tara kudin shiga kimanin Dala miliyan 500 daga kudaden tikiti da kuma lasisin haska gasar a talabijin da kuma tallace-tallace da sauransu.
Yadda za a ba da tikitin
A ranar 19 ga wan Janairu ne FIFA ta bude neman tikitin kallon gasar Qatar 2022 na tsawon kwana 20, wanda aka rufe a ranar Talata, gabanin bayar da tikitin ta hanyar kuri’a ta kwamfuta.
Hukumar ta bayyana cewa a ranar 8 ga watan Maris za ta sanar da wadanda suka samu nasarar samun tikicin shiga kallon gasar.
Ta ce za a sayar da tikitin ne ta hanyar bayar da fifiko ga wadanda suka riga bayyana bukatarsu.
Mazauna kasar Qasar, ciki har da ma’aikata mazauna kasar za su samu garabar tikitin Dala 11 domin kallon kananan wasannin gasar.