✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Super Eagles ta gamu da cikas a ƙoƙarin neman tikitin Gasar Kofin Duniya

Wasan da Nijeriya za ta yi Bafana Bafana a watan Satumba, zai kasance mai matuƙar muhimmanc.

Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta gamu da cikas a ƙoƙarinta na neman yankar tikitin shiga Gasar  Kofin Duniya ta baɗi, bayan da ta tashi canjaras 1-1 da Zimbabwe.

Victor Osimhen ne ya fara ci wa Nijeriya kwallo a minti na 74 a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom.

Sai dai Zimbabwe ta farke ana daf da tashi a minti na 90 ta hannun ɗan wasanta na gaba, Taranda Chirewa.

Wannan sakamako na nufin cewa Nijeriya na matsayi na huɗu a rukunin C, inda Ghana ke gabanta a matsayi na ɗaya da kusan ratar maki shida bayan buga wasanni shida.

Wasan da Nijeriya za ta yi Bafana Bafana a watan Satumba, zai kasance mai matuƙar muhimmanci, la’akari da cewa ƙasar da ke saman kowane rukuni ne kaɗai ke samun damar zuwa Gasar Kofin Duniya.

A ranar Juma’a ce tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta doke Rwanda da ci 2-0 a birnin Kigali a wasannin neman gurbin shiga Gasar Kofin Duniya.

Ɗan wasan Nijeriya Victor Osimhen ne ya zura duka ƙwallayen biyu gabanin hutun rabin lokaci.

A lokacin Nijeriya ta koma matsayi na huɗu a cikin ƙasashe shida da ke Rukunin C bayan wasanni biyar-biyar.

Ƙasar da ta zama ta farko a kowane rukuni daga cikin rukunai tara na ƙasashen Afirka ne ke da tabbacin shiga gasar kofin na duniya, wanda a karon farko aka faɗaɗa zuwa ƙasashe 48.

Sai kuma za a zaɓi ƙasashe huɗu da suka fi ƙoƙari daga cikin waɗanda suka zama na biyu, sai su fafata wasan kifa-ɗaya-ƙwala na neman cike gurbi, inda waɗanda suka samu nasara za su iya samun damar shiga gasar.

Sauran wasannin da suka rage wa Super Eagles su ne na ranar 1 ga Satumba wanda Nijeriya za ta yi da Rwanda sai na ranar 8 ga Satumba tsakaninta da Afirka ta Kudu da kuma na ranar 6 ga Oktoba da za ta fafata da  Lesotho sai cikon na ƙarshe wanda za ta yi karon batta da Benin a ranar 13 ga Oktoba.