Manyan masu tsaron bayan Faransa, Raphael Varane da Ibrahima Konate, sun kamu da rashin lafiya a jajibirin karawar kasarsu da Ajentina a wasan karshe na Gasar Kofin Duniya ta 2022.
Akwai yiwuwar Faransa, mai kokarin kare kambunta a gasar, ba za ta yi amfani da manyan masu tsaron bayan ba, ko kuma daya daga cikinsu, kamar yadda majiyoyi ke hasashe.
- Za A Haramta TikTok A Ma’aikatun Amurka
- Dan haya ya kashe abokinsa kan N300
- Batanci: Mun yaba da hukuncin rataye Abduljabbar —Majalisar Malamai
Kafar labaran wasanni ta ESPN ta ruwaito majiyoyi na cewa Ibrahima Konate ba ya fita daga dakinsa saboda rashin lafiya, Raphael Varane kuma akwai alamar rashin lafiya a tare da shi.
Wannan cikas din na zuwa ne a yayin da Faransa ke bukatar nasara a wasan karshen domin ta cin kofin a karo na uku da kuma kafa tarihin zama kasar da ta kare kambunta a shekara 60 da suka gabata.
Tun a jajibirin gasar da ke gudana a kasar Qatar, rauni ya hana manyan ’yan wasan Faransa, Paul Pogba, N’Golo Kante, Karim Benzema, Presnel Kimpembe, Lucas Hernandez da Christopher Nkunku, shiga gasar.
Mun dauki mataki —Deschamps
Da yake magana kan rashin lafiyar ’yan wasan nasa, kocin Faransa, Didier Deschamps, ya ce tun lokacin da rashin lafiya ya hana Dayot Upamecano da Adrien Rabiot buga wasan kusa da karshe, tsakaninsu da Maroko, kasar ta dauki matakan hana yaduwar cutar zuwa sauran ’yan wasan.
Ko da yake, wasu majiyoyi sun shaida wa ESPN cewa Rabiot da Upamecano suna samun sauki kuma Deschamps ya tabbatar cewa akwai yiwuwar za su buga wasansu da Ajentina ranar Lahadi.
Ya ce, “Dayot zai iya buga wasa, ko da yake daga ranar Asabar sai da ya kwana uku yana fama da zazzabi da rashin kuzari… Ganin zafin wasan ne na bar shi na sa Konate wanda ya yi rawar gani.
“Rabiot ma ba shi da lafiya amma yau ya samu sauki, sai dai bai murmure ba, shi ya sa muka ce ya zauna a daki ya huta. Mun huta na kwana hudu a jere, don haka zai iya yin wasa ranar Lahadi.”
Ajentina ba kanwar lasa ba ce
Ajentina dai ba kanwar lasa ba ce, kuma ita ma tana son daukar kofin a karo na uku.
Uwa uba wannan shi ne karon karshe da babban dan wasan Ajentina mai shekara 35 kuma Gwarzon Dan Wasan Ballon d’Or, Lionel Messi zai fito a gasar.
Hasali ma, Messi wanda shi ne Kyaftin din Ajentina, ba zai so ya zama ya kammala gasar da rashin nasara ba, ga shi kuma wannan ce damarsa ta karshe ta samun kofin.
A halin yanzu, Messi ba shi da burin da ya wuce cin Kofin Duniya, wanda a tarihin rayuwarsa, sau biyar ke nan yana buga Gasar Kofin Duniya ba tare da kasarsa ta ci kofin ba.
Idan ya yi nasara, to zai zaman dan kwallon da babu kamarsa a tarihin tamola, kuma zai zame wa Ajentina Maradona na biyu.
Ba mu karaya ba —Dembele
Amma duk da haka, da yake magana kan rashin lafiyar a ranar Juma’a, dan wasan Faransa, Ousmane Dembele, ya ce, “Kwayar cutar ba da karya mana gwiwa ba.”
Ya kara da cewa ’yan wasan da rashin lafiya ya hana bugawa a wasan Kusa da Karshe da suka yi da Maroko, “Dayot da Adrien sun yi fama da ciwon ciki, amma sun samu sauki, kuma ina fata kowa zai samu cikakkiyar lafiya kafin wasan karshen.”
Dembele ya ce, “Adrien ya samu sauki kuma ina ganin kowa zai samu cikakkiyar lafia, kuma mun dauki matakan kariya.
“A ranar farko, Dayot ya zauna ne a daikinsa, mu muka kawo masa abinci, amma washegari ya wartsake.”
Kungiyar Kwallon kafa a Les Bleus a Faransa dai na neman zama kasa ta farko da ta kare kofinta a cikin shekara 60 da suka gabata, tun bayan da Brazil ta yi hakan a shekarar 1962.