Sa’o’i kadan kafin fara Gasar Kofin Duniya ta Qatar 2022, Faransa ta sanar cewa dan wasanta, Karim Benzema, wanda ya lashe gasar Gwarzon dan Kwallon Kafa na Duniya ta Ballon D’Or, ba zai samu buga wasa ba.
Faransa, mai rike da kambun Kofin Duniyar, ta sanar cewa Benzema zai tafi hutu na sati uku, sakamakon raunin da ya kara samu a cinya a wurin atisaye a Qatar ranar Asabar.
- Qatar 2022: FIFA ta nada Sunday Oliseh a kwamitin kwararrunta kan Kofin Duniya
- Qatar 2022: Darajar Kofin Kwallon Kafa Na Duniya
Bayan raunin ya sa shi fita daga atisayen a kasar Qatar da ke karbar bakuncin gasar, Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa ta ce, sakamakon raunin, Benzema, “Zai tafi hutu na tsawon mako uku domin ya samu ya murmure.”
Yayin da Faransa ke kokarin mai maye gurbin dan wasan kafin wasanta na farko da kasar Australia a ranar Talata, da wuya Benzema ya samu buga wasa a gasar Kofin Duniya ta Qatar 2022 da ke karewa a ranar 18 ga watan Disamba.
Kasar na da burin kafa sabon tarihi a Gasar Kofin Duniya ta 2022 ta hanyar kare kambunta, wanda rabon da hakan ta faru tun shekarar 1962 da Brazil ta kare kambunta.
Sai dai tun da farko ta sanar cewa manyan ’yan wasanta — na tsakiya Paul Pogba da N’Golo Kante — ba za su buga mata gasar ba.
Golanta na biyu Mike Maignan da dan wasan tsakiya Presnel Kimpembe da dan wasan baya RB Leipzig da dan wasan gaba Christopher Nkunku sun janye sakamakon raunukan da ssuka samu gabanin zuwan tawagar kasar zuwa Qatar.
Kocin tawagar Faransa, Didier Deschamps, ya ce, “Na ji wa Karin Benzema takaici, ganin cewa yana da babban buri game wa gasar Kofin Duniya ta bana.”
Wannan yananyi ya kara kawo cikas ga Faransa mai neman kare kambunta, inda take ta fadi-tashin neman wanda zai maye gurbin dan wasan mai shekara 34, a gasar da ake farawa a ranar Lahadi.
Kasar za ta fafata a rukunin D da kasashen Australia Denmark da Tunisia amma kocinta ya ce, “Duk da wannan gagarumar matsala da tawagar Faransa ta samu, ina da kwarin gwiwa game da ’yan wasan. Kuma za mu yi iya bakin kokarinmu domin tunkarar kalubalen da ke gabanmu.”
Tun a watan Oktoba dai dan wasan na kungiyar Real Madrid yake ta fama da rauni a cinyarsa, wanda ya sa bai buga samu buga kimanin rabin wassani shida na karshe da kungiyar ta yi ba.
A bisa dokar Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), kocin Faransa, Deschamps, zai iya maye gurbin dan wasan da ya samu rauni, daga yanzu zuwa ranar Litinin.