Tawagar ’yan wasan kasar Argentina ta tsallaka zuwa Matakin Kusa na Karshe bayan ta kwaci kanta da kyar a hannun Netherlands wasan Kwata-Fainal na Gasar Kofin Duniya na Qatar 2022.
Argentina ta kai bantenta ne bayan bugun fanareti a wasan da ya dauki hankali matuka, wanda kasashen biyu suka tashi canjaras da ci 2-2.
- Qatar 2022: Croatia ta cire Brazil a bugun fanareti
- Qatar 2022: Croatia ta cire Brazil a bugun fanareti
Netherlands ta gamu da ajalinta a Gasar Kofin Duniya na Qatar 2022 a hannun Argentina ne bayan ta yi nasara a wasanni 15 na Gasar Kofin Duniya — inda take kan gaba da kwallaye biyu.
Kafin wasan na daren 9 ga watan Disamba, 2022 da Netherlands ta yi rashin nasara, ta lashe wasanni 19 karkashin jagorancin kocinta, Louis Van Gal.
Kwallayen da aka zura
Nahuel Molina na Argentina ne ya fara zura kwallo a ragar Netherlands a minti na 35, kafin a minti na 73, Lionel Messi ya kara na biyu a bugun daga kai sai gola.
Wannan kwallon da Messi ya zura ita ce ta 2,700 a tarihin Gasar Kofin Duniya.
A minti na 83 dan wasan Netherlands, Wout Weghorst ya farke kwallon farko, sannan ana dab da bisa usur din tashi ya farke ta biyun — aka tashi 2-2.
A sakamakon haka aka tafi karin lokaci amma har ya kare babu bangaren da ya kara ci.
Da hakan aka tafi bugun daga kai sai gola, inda Argentina ta ci duk kwallayenta hudu, Netherlands kuma ta ci uku.
Yanzu ta tabbata, a matakin Semi-Fainal Argentina za ta kara da kasar Crotia, wadda ta doke Brazil a matakin Kwata-Fainal.
Maimaita tarihi
Karo na biyar ke nan a tarihi da Argentina take kaiwa matakin Kusa Da Na Karshe a Gasar Kofin Duniya, bayan shekarar 1930, 1986, 1990 da kuma 2014.
Karo na biyar kuma ke nan kuma da ta yi nasara a bugun daga kai sai gola da aka yi da ita a gasar cin Kofin Duniya.