Wasan Karshe na Gasar Cin Kofin Duniya na 2022 ba tsakanin Faransa da Argentina ba ne kawai, tsakakin manyan ’yan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta PSG ne — inda Lionel Messi shi ne Kyaftin din Argentina, Mbappe kuma ke bangaren Faransa a matsayin dan wasa.
Za a buga wasan karshe na gasar da ke gudana a kasar Qatar ne ranar Lahadi, inda kowanne daga manyan ’yan wasan da kuma kasashensu ke neman kafa tarihi, bayan shafe mako hudu kasashe 32 suna fafatawa a wasanni 64 na gasar.
- Qatar 2022: Final-Ajantina Da Faransa
- Sabbin takardun kudin da CBN ya fitar sun kare tatas a bankuna
Neman kafa tarihi
A yayin da ake tsimayen ganin wanda zai je gida da kofin gasar, wadda ita ce karo na 22 tun da aka fara ta shekara 92 da suka gabata (1930), hankalin masu sharhi kan harkar kwallon kafa da ’yan kallo ya koma kan fitaccen dan wasan nan na PSG Lionel Messi da takwaransa shi ma na kungiyar, Kylian Mbappe.
Messi mai shekara 35 na fatan ya lashe Kofin Duniya don kafa tarihi irin na Maradona, shi kuwa Mbappe na son kare kambun da suka lashe a 2018 a Kasar Rasha.
Duk da cewa ’yan wasa 22 ne za su kasance a filin wasa daga kasashen biyu, Mpabbe da Messi na neman shan gaban juna wajen samun Takalmin Zinare da zama zama Gwarzon Dan Wasa a gasar, kasancewar kawo yanzu kowannensu na da kwallo biyar a gasar.
Wa za a bari a baya?
Amma, idan har aka kammala gasar babu wanda ya wuce wani yawan kwallo a cikinsu, za a duba wanda ya fi yawan taimakawa a ci kwallo — wanda Messi ne ke gaba da adadin taimakawa guda uku, Mbappe kuma ke da biyu.
Messi ya kafa tarihin zama dan wasan da ya fi jefa wa Argentina kwallaye a Gasar Cin Kofin Duniya, inda yake da kwallo 11 a zango biyar da ya buga gasar, shi kuwa Mbappe yana da kwallo tara daga gasar sau biyu da ya taba bugawa a rayuwarsa.
Tabbas wasan zai dauki hankali, ganin yadda kasashen biyu wadanda kowaccensu sau biyu tana cin kofin a baya, (Argentina a 1978 da 1986 dai kuma Faransa a 1998 da 2018) ke neman zarce dayar da na uku.
Za a buga wannan wasa ne a Filin Wasa na Lusail da ke Qatar, wanda ya ke cin adadin mutane dubu 90.
Amma, idan Mbappe da Faransa mai rike da kofin suka ya nasara, ba gaban Argentina kawai Faransa za a sha wajen yawan kofi ba, za kuma ta shiga jerin kasashen da suka kare kambun gasar.
Kazalika, Mbappe na da kofi biyu, kuma ya hana Kyaftin Lionel Messi cin Kofi Duniya a tarihin rayuwarsa.
Sau biyar Messi yana buga gasar (2006, 2010, 2014, 2018 da 2022) kuma wannan ne damarsa ta karshe ta cin kofin, tun da ya riga ya tabbatar cewa ba zai buga gasa ta gaba ba.
Zaratan ’yan wasa
Sai dai akwai sauran ’yan wasa 20 da za su iya bada mamaki wajen jagorantar kasar da za ta lashe kofin.
Olivier Giroud na Faransa mai shekara 36 ya kafa tarihi a gasar, inda ya zama dan wasan da ya fi jefa wa Faransa kwallo a raga a tarihinta.
Julian Alvarez: Matashin dan wasa Argentina ne da tauraronsa ke haskawa kuma zuwa yanzu yana da kwallo hudu a gasar. Kuma shi ne dan kuma wasan da ya yi waje da kasar Croatia a matakin kwata fainal inda ya jefa kwallo biyu a raga.
Antoine Griezmann: Dan wasa ne da ya jagoranci Faransa har zuwa wasan karshe na gasar. Ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar da kasar ta samu.
Enzo Fernandez: A iya cewa kasar ta samu albarka wajen samun wannan dan wasa. Don kuwa shi ne ke jan zarensa yadda yake so a tsakiyar fili a duk lokacin da Argentina ke murza leda.