Shugaban Rasha Vladimir Putin ya jajanta kan mutuwar shugaban kamfanin sojojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin, wanda tsohon mai dafa masa abinci ne.
A wani jawabi da ya gabatar a talabijin, Putin ya ce kamfanin Wagner ya ba da gagarumar gudunmawa ga Rasha a Ukraine.
- Salah zama daram a Liverpool — Klopp
- Nijar ta ba sojojin Mali da Burkina Faso izinin kawo mata dauki
Putin ya kara da cewa Rasha za ta yi bincike kan lamarin da ya jawo hatsarin jirgin da a cikinsa Prigozhin ya rasa ransa, tare da mutum tara a Rasha a ranar Laraba.
Putin ya mika sakon ta’azziyarsa ga iyalan mutanen da suka mutu a hatsarin da ya faru a yankin Tver, mai nisan kilomita 200 daga birnin Moscow a Arewa maso Yamma.
A cewar Putin, Prighozin “dan kasuwa ne mai basira, wanda ya san shi tun shekarun 1990.”
Putin ya ci gaba da cewa Prigozhin mutum ne da ya dinga “haduwa da kaddarar rayuwa wanda kuma ya aikata kura-kurai a rayuwarsa.”