✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nijar ta ba sojojin Mali da Burkina Faso izinin kawo mata dauki

Mali da Burkina Faso sun yaba da damar da Janar Tchiani ya ba sojojinsu na kawo wa Nijar daukin gaggawa

Shugaban Gwamnatin Sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya sanya hannu a takardar bai wa sojojin Mali da Burkina Faso damar kawo dauki a duk lokacin da aka kawo wa kasarsa hari.

Janar Tchiani ya sanya hannun ne a ranar Alhamis, a lokacin da Ministan Harkokin Wajen gwamantin sojin Burkina Faso, Olivia Rouamba da takwaransa na Mali Abdoulaye Diop, suka ziyarci birnin Yamai, inda suka tattauna da shi.

Mataimakin Sakatare-Janar na Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijar, ya sanar a cikin wata takarda cewa Mali da Burkina Faso sun yaba da sanya hannun da Janar Tchiani ya yi, domin ba wa dakarun kasashensu damar, “kai wa Nijar dauki idan aka kawo mata hari.”

Juyin mulkin da Janar Tchiani ya yi wa Shugaba Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli ya sa kungiyar ECOWAS katse hulda da kasar tare da barazanar dawo da shi da karfin soji.

Nijar ce kasa ta hudu a yammacin Afirka da sojoji suka yi juyin mulki daga shekarar 2020, bayan Burkina Faso, Guinea da Mali.

Gwamnatocin sojin Burkina Faso da Mali sun yi wa Nijar alkawarin kawo mata dauki da kuma yakar duk kasar da ta kawo mata hari.

A ranar Asabar Janar Tchiani ya yi gargadin cewa duk kasar da ta kawo wa Nijar hari, to za ta gane cewa shayi ruwa ne.