Rikicin da ake fuskanta tsakanin Rasha da Ukraine ya dauki sabon salo ranar Litinin bayan da Shugaba Vladimir Putin ya ba Ma’aikatar Tsaron kasarsa umarnin tura dakarunta zuwa cikin kasar Ukraine.
A cewar Shugaban na Rasha, dakarun dai za su shiga kasar ne don su yi aikin kiyaye zaman lafiya a yankunan Donetsk da Luhansk.
- Babban Taron APC: Abin da ya sa Kwamitin Buni ke jan kafa
- NAJERIYA A YAU: Yadda kwadayi ke jefa masu daukar albashi cikin garari a Najeriya
A cewar sabuwar dokar da aka fara wallafa ta ranar Talata, Putin ya ce Rasha za ta amince da cin gashin yankunan biyu a matsayin kasashe.
Dokar ta ce dakarun za su yi aikin kiyaye zaman lafiya ne a iyakokin har zuwa lokacin da yankunan biyu za su sasanta da juna.
Jaridar Financial Times ta rawaito cewa Fadar White House ta ce Shugaba Joe Biden ya ce Amurka kwanan nan za ta kakaba wa Rasha sabon takunkumi da ma yankunan na Luhansk da Donetsk.
Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Liz Truss ma ya ce “Nan ba da jimawa ba za mu sanya wa Rashar takunkumin saboda karya dokokin kasa da kasa da suka yi ta hanyar kutsa iyakar Ukraine da ’yancinta a matsayin kasa,” kamar yadda ta wallafa a shafin Twitter.
Tuni dai kungiyar kawancen tsaro ta NATO ita ma ta yi gargadin cewa matakin na Putin zai kawo koma baya wajen tattaunawar da ake kokarin yi don samar da zaman lafiya a yankin, yayin da shi kuma Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya yi kira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya gaggauta zama a kan lamarin don taka wa Rashan birki.