✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Pique ya rasa mabiya miliyan 1 a Instagram bayan rabuwa da Shakira

Dan wasan na ci gaba da rasa mabiya a Instagram

Fitaccen dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Gerard Pique, ya rasa mabiya miliyan daya a shafinsa na Instagram, bayan ya rabu da matarsa, kuma shahararriyar mawakiya, Shakira.

A baya-bayan nan ma dan wasan na Barcelona ya rasa mabiya miliyan biyar a shafin na Instagram.

A kullum shafin nasa na Instgram na ci gaba da fuskantar zaizayar mabiya, yayin da ita kuma tsohuwar matar ta shi, Shakira ke samun mabiya kusan 300,000 a kullum.

An rawaito dan kwallon kafar da mawakiyar sun raba aurensu ne bayan da Shakira da kama shi da wata mata yana cin amanarta.

Tuni wani bincike da jaridar Culemania ta yi na jin ra’ayin magoya baya, kaso 63 cikin 100 ya nuna yadda magoya bayan Barcelona ke son dan wasan ya yi ritaya ko ya bar kungiyar.

Kaso 17.1 ne kadai suka nuna sha’awar dan wasan ya ci gaba da murza leda a Barcelona.

Kazalika, kaso 14,1 sun bayyana cewar dan wasan na iya ci gaba da zama a kungiyar matukar yana da ishasshiyar lafiya.

Yayin da kuma kaso 5.4 suka bayyana ra’ayin cewar dan wasan ya jingine takalmansa.

Ita kuwa Shakira tuni ta samu gwaggwabar riba, inda mabiya miliyan biyu suka kwaroro tare da karuwa a shafin nata na Instagram, bayan rabuwar.