✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Philip Lahm bai gamsu da yadda ake gudanar da Gasar Gwarzon dan kwallon Duniya ba

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da ke Jamus Philip Lahm ya yi kira ga Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da ta…

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da ke Jamus Philip Lahm ya yi kira ga Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da ta canza tsarin da take bi wajen fitar da Gwarzon dan kwallon Duniya (Ballon D’ Or) a kowace shekara.
Ya ce idan aka yi la’akari da yadda ake ba wadanda ke buga kwallo a bangaren gaba (Strikers) fifiko wajen lashe gasar fiye da sauran ’yan kwallo to akwai bukatar a sake tsari.
dan kwallon ya ce yakamata a kirkiro da gasar dan kwallon duniya a bangaren tsakiya (Midfielders) da bangaren baya (defenders) da kuma a bangaren masu tsaron gida (Goalkeepers).  Ya ce hakan ce za ta sa kowane dan kwallon ya san ana damawa da shi.
Ya ce tsarin da ake bi a halin yanzu na zabar ’yan kwallon gaba da suke kasancewa Gwarzon dan kwallon duniya a shekara da shekaru sam bai gamsar da shi ba, don haka akwai bukatar a sake bullo da sabon tsari da zai game kowane bangare.
Sai dai haifaffen Jamus Lahm ya yaba wa shahararren dan kwallon FC Barcelona Lionel Messi a kan nasarar da ya samu na lashe gasar har sau biyar.
Ya bayyana gasar a matsayin tamkar wacce ’yan kwallon gaba (strikers) ne kadai ke fafatawa a kanta.