✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Peter Obi ya kai wa Wike ziyara

Ganawar Obi da Wike ita ce karo na biyu tun bayan da aka soma buga kalangun tunkarar Zaben 2023.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya kai wa Gwamnan Jihar Ribas, Nyemsom Wike ziyara a wannan Juma’ar.

Aminiya ta ruwaito cewa, gwamnan ya karbi bakuncin dan takarar Shugaban Kasar ne a wani gidansa na Rumupeirikom da ke kan titin Ada George a Fatakwal, babban birnin jihar.

Sai dai babu tabbaci dangane da dalilin wannan ziyara da dan takarar ya kai wa gwamnan wanda akwai bambancin shekar siyasa a tsakaninsu.

Ganawar dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar PDP ke kokarin shawo kan Gwamna da sulhunta rikicin cikin gida da ke tsakanin da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.

Rahotanni sun bayyana cewa, ganawar Peter Obi da Gwamna Wike ita ce karo na biyu tun bayan da aka soma buga kalangun siyasa domin tunkarar babban zabe na shekara mai zuwa.

Ana dai zargin cewa, ziyarar ba za ta rasa nasaba da kokarin da Peter Obi ke yi ba na ganin gwamnan ya goyi bayan takararsa ta shugabancin kasar.