✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Pele: Gwarzon Dan kwallon Kafa Na Duniya Ya Rasu

Ana ganin Pele a matsayin dan wasan kwallon kafa da ba a taba yin kamarsa ba a tarihi.

Shahararren dan wasan kwallon kafa na Duniya, Pele, ya rasu yana da shekara 82 a duniya.

Kawo yanzu, Pele wanda ya rasu ranar Alhamis bayan fama da jinya, shi ne dan kwallon kafa tilo da ya lashe Gasar Kofin Duniya sau uku a rayuwarsa.

Da take sanar da rasuwarsa, ’yarsa, Kely Nascimento, ta ce, “Babu abin da za mu ce maka sai godiya. Kaunarmu gare ka ba ta da iyaka. Huta lafiya”

Manajansa, Joe Fraga, ya tabbatar da rasuwar, yana mai cewa: “Sarki ya riga mu Gidan Gaskiya.”

Pele, wanda bakar fata ne dan kasar Brazil, ya fara lashe Gasar Cin Kofin Duniya ne tun yana shekara 17 a duniya.

A halin yanzu, ana ganin sa a matsayin dan wasan kwallon kafa da ba a taba yin kamarsa ba a tarihi.

Yana kuma cikin jerin mutane 20 bakaken fata da suka fi shahara a duniya a Karni na 20.