Kwamitin tuntuba da jam’iyyar PDP ta kafa, ya bayar da shawarar cewa jam’iyyar ta yi watsi da watsi da tsari karba-karba yayin tsayar da dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.
A madadin haka, kwamitin ya yi kira da jam’iyyar ta duba cancanta maimakon tsarin karba-karba da a baya ta rika amfani da shi.
- ’Yan bindiga: Sheikh Gumi yana mana katsalandan – Masari
- Ba sace ni aka yi ba, guduwa na yi – Amaryar Kano
Gwamnan Bauchi Bala Muhammad wanda shi ne jagoran kwamitin mai mutum 14, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake gabatar da rahoto ga shugabannin jam’iyyar a shelkwatar da ke birnin Abuja.
Wasu mambobin kwamitin sun ce duk da cewa akwai wadanda ke ganin ya kamata a fifita yankunan Arewa maso Gabas da Kudu maso Yamma, kowane dan Najeriya yana da ’yancin a ba shi takara karkashin inuwar jam’iyyar matukar an yi la’akari da cancantarsa.
Aminiya ta samu cewa an kafa kwamitin ne domin manufar gano dalilin da ya sanya jam’iyyar ta sha kasa a yayin zaben 2019 da kuma manufar bayar da shawarwarin da suka dace da zai kai ta ga ci a 2023.
Ana iya tuna cewa, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar jam’iyyar PDP ta tsayar a zaben 2019, inda Shugaba Muhammadu Buhari ya tika shi da kasa.