Tsohon Shugaban kasa a zamanin mulkin soji Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce babbar jam’iyyar adawa ta PDP tana da bangaren soji, wanda mambobinsa ya kunshe wadansu manyan Janar-Janar.
Janar Babangida ya ce manyan mambobin bangaren sojin sun hada da shi kansa da Laftana Janar Theophillus Yakubu danjuma da Janar Olusegun Obasanjo da Laftana Janar Aliyu Mohammed da sauransu.
Janar Babangida ya bayyana haka ne a ranar Asabar da ta gabata, lokacin da yake karbar rahoton kwamitin riko na Sanata Ahmed Makarfi kan “dabaru da harkokin cikin gidan jam’iyyar” a karkashin jagorancin Farfesa Jerry Gana a gidansa da ke Minna a Jihar Neja, inda Janar Babangida ya ce: “Mu ne bangaren soji na PDP, muna da babbar sha’awa a cikin PDP.”
Tsohon Shugaban kasar ya alkanta kafuwar jam’iyyar da mataki irin na sojin Jamhuriyyar Ireland, inda ya ce: “Na rada wa kanmu sunan bangren sojin IRA na Jam’iyyar PDP; kuma nag ode ASllah, mu ne muka zo da batun cewa PDP za ta yi shekara 60 tana mulki.” Janar Babangida ya kuma nanata yakininsa na cewa tsarin jam’iyyun biyu ya fi dacewa da Najeriya, inda ya ce suna bayar da zabi ga jama’a.
Ya ce yana da yakinin idan jam’iyyar ta magance rigingimunta, za ta iya mulkin Najeriya na shekara 60, kuma ya bayyana cewa yana da yakinin za ta fice daga halin da take ciki ta fito da karfinta.
Tsohon Shugaban Sojin ya dade bai yi magana a bainar jama’a ba kan harkkokin jam’iyyarsa wadda take fama da rarrabuwa tun lokacin da ta sha kaye a hannun Jam’iyyar APC a zaben shekarar 2015.
Jam’iyyar PDP tana fama da takaddama a gaban kotuna inda a mako biyu da suka gabata Kotun daukaka kara ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar ga Sanata Ali Modu Sheriff, hukuncin da kwamitin riko na Sanata Ahmed Makarfi ya ce zai kalubalanta a gaban Kotun koli.
Janar Babangida ya ce PDP ce kawai jam’iyyar da ta karbu a sassan kasar nan kuma ana jin samuwarta a kowane bangare na kasa.
PDP tana da bangaren soji – Babangida
Tsohon Shugaban kasa a zamanin mulkin soji Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce babbar jam’iyyar adawa ta PDP tana da bangaren soji, wanda mambobinsa ya…