Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta ce saba wa matakan kariyar COVID-19 da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi yayin sabunta rajistarsa ta jam’iyyar APC abun kunya ne a gare shi.
PDP ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, wadda ta ce abin da Buhari ya aikata abun kunya ne.
- Buhari ya sabunta rajistarsa a jam’iyyar APC
- Buhari ya koma Daura don yin rajistar APC
- PDP ta bukaci Kotun ICC ta hukunta tsoffin Hafsoshin Tsaro
Jam’iyyar ta ce rashin kiyaye dokokin da mahukuntan lafiya suka shar’anta domin dakile yaduwar annobar Coronavirus da Shugaba Buhari ya yi babban abun kunya ne.
“Tabbas abun kunya ne a ce a yayin da ’yan Najeriya ke kokarin kiyaye matakan kariyar COVID-19, amma Shugaban kasa ya karya dokar yayin da yaje sabunta rajistar jam’iyyarsa a Daura, Katsina.
“Kafofin sadarwa sun nuna yadda hotunan shugaban kasa suka karade yana tattaunawa da shugabannin jam’iyyarsa, ba tare da takunkumi ba, bare bayar da tazara,” a cewar PDP.
Jam’iyyar ta kara da cewa babban abun kunya ne ga shugaban da yanke hukuncin wanda ya karya dokar matakan kariya, a kuma same shi ya karya su kwanaki biyar bayan sanya wa dokar hannu.
A ranar Asabar ne Shugaba Buhari ya sabunta rajistarsa ta jam’iyyar APC, a mazabar Sarkin Yara da ke garin Daura a jihar Katsina.