✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PDP ta yi wa Buhari martani kan yunkurin fashi a Fadar Gwamnatin Najeriya

Dole ne Buhari ya sake fasalin yanayin matakan tsaro a cewar PDP.

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP, ta ce yunkurin yin fashi a kusa da Fadar Gwamnatin kasar ya nuna gazawar Shugaba Muhammadu Buhari wajen samar da tsaron da Najeriya bukata ba.

PDP ta yi wannan furuci ne a matsayin martani kan yadda wasu bata gari suka yi yunkurin shiga gidan Shugaban Ma’aikatan Fadar gwamnatin tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari, da ke Villa.

Cikin wani jawabi da mai magana da yawun jam’yyar Kola Ologbondiyan ya fitar, PDP ta  ce “Duk duniya kowa ya san Fadar Shugaban Kasa, nan ake da dukkanin wasu bayanai da ya kamata a ba su cikakken tsaro.

“Don dukkan wani yunkuri na kutse na iya kawo tangarda ga al’amuran tsaro baki daya.

“A watan Yunin shekarar da ta gabata ma an yi rikici a Fadar Gwamnatin Kasar inda aka yi harbe-harbe a tsakanin jami’an tsaron iyalan shugaban kasa.

“Jam’iyyarmu na cikin kaduwa da damuwa cewar Buhari ba zai iya samar wa da fadar shugaban kasa da Najeriya tsaron da ake bukata ba.

“Don haka, muna kira ga Buhari da ya tashi haikan, wajen yi wa tsarin tsaron kasar garambawul, ba wai yake nuna damuwa a jikinsa ba,” a cewar Kakakin jam’iyyar.

Tuni dai wannan yunkuri na shiga gidan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya dauki hankulan mutane da dama, inda masana suka shiga yin sharhi kan lamarin.

Aminiya ta ruwaito cewa, Fadar Shugaban Najeriya ta tabbatar da abin da ta kira yunkurin da wasu suka yi na fasa gidan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ranar Litinin.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, ta ce wasu sun yi yunkutin fasa gidan Farfesa Ibrahim Gambari da misalin karfe uku na dare.

Sanarwar ta ce gidan nasa yana kusa da fadar shugaban kasa sai dai yunkurin da aka yi na fasa gida bai yi nasara ba.