Jam’iyyar PDP, ta sake ɗage taron Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) zuwa ranar 28 ga watan Nuwamba 2024.
A baya jam’iyyar ta shirya gudanar da taron ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Oktoba.
- Za mu bar Nijeriya idan ba a bari mun ƙara kuɗin kiran waya ba —MTN
- Ambaliya: Masarautar Kaltungo ta bai wa Borno tallafin kayayyaki
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP, ya sanar da ɗagewar bayan wata tattaunawa da Kwamitin Amintattu a daren Talata, a Abuja.
Gwamnan ya bayyana cewa an ɗage taron ne don bai wa jam’iyyar ƙarin lokaci don mayar da hankali kan zaɓen gwamna da za a yi a Jihar Ondo a ranar 16 ga watan Nuwamba.
Wannan shi ne karo na uku da jam’iyyar ke ɗage taron.
Da farko an tsara gudanar da taron ne a watan Agusta, sai aka ɗage zuwa watan Satumba, daga baya kuma aka sake ɗagewa zuwa ranar 24 ga watan Oktoba.
Ya ce, “Bayan tattaunawa tsakanin sassa daban-daban na jam’iyyar PDP, jam’iyyar ta yanke shawara.
“Taron Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) da aka tsara gudanarwa a ranar 24 ga watan Oktoba 2024, an mayar da shi zuwa 28 ga watan Nuwamba 2024.”
Ya ce sun ɗage taron ne don tabbatar da cewa jam’iyyar ta yi shirin da ya dace domin tunkarar zaɓen gwamna na Ondo da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba 2024.
Taron ya kuma jaddada buƙatar haɗin kai, inda aka yi kira da ’ya’yan jam’iyyar da su guji kalaman da za su iya haifar da rabuwar kai.
Jam’iyyar PDP ta ayyana babban muradinta na ganin ta ƙwaci mulki a zaɓen 2027.