✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta mayar wa Sanata Ibrahim Mantu martani

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta ce ba da yawunta ne Sanata Ibrahim Mantu ya rika jirkita sakamakon zabe ba, kuma ta ce ba ta…

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta ce ba da yawunta ne Sanata Ibrahim Mantu ya rika jirkita sakamakon zabe ba, kuma ta ce ba ta taba umartar wani dan jam’iyyar ya yi mata magudin zabe ba.

Jam’iyyar PDP ta nesanta kanta daga kalaman na Sanata Mantu ne, inda ta ce batun bai shafi jam’iyyar ba kamar yadda sanarwar da ta fito daga ofishin Babban Sakataren Jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ta nuna. Sakataren ya ce Mantu ya yi magana ne game da abubuwan da ya yi bisa radin kansa a zabubbukan da suka shiga. “Ba mu taba sa wani dan PDP ya yi magudin zabe ba,” inji shi.

“Mutane suna tsayawa takara a karkashin jam’iyyu yayin zabe. A Jam’iyyar PDP muna ba dan takara littafin da ya kunshi dokokin zabe da yadda zai yi yakin neman zabe. Amma babu wurin da za mu umarce shi ya yi magudin zabe a madadin jam’iyya. Idan wani dan takara ya saba wa dokokin zabe, ya yi magudin zabe. To ya yi haka ne bisa radin kansa, amma ba bisa umarnin jam’iyyarmu ba. Idan haka ta faru, ba za a dora wa jam’iyyar laifi ba,” inji Sakataren.

Sanata Mantu, wanda toshon dan Majalisar Dattawa ne, kuma jigo a Jam’iyyar PDP a lokuta da dama an zarge shi da hannu wajen cuwa-cuwar siyasa, ciki har da zargin yunkurin sauya kundin tsarin mulkin kasa ta yadda zai bai wa tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo damar yin ta-zarce a karo na uku.