✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta lashi takobin hukunta Wike kan yi mata zagon kasa

PDP ta kafa kwamitin bincike kan abubuwan da suka faru da ita a 2023.

Jam’iyyar PDP ta sha alwashin hukunta tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da wasu ’ya’yanta kan yi mata zagon kasa a zaben 2023.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai a ranar Talata, mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Ambasada Umar Damagum ya bayyana cewa baya ga Nyesom Wike, akwai wasu ’ya’yan jam’iyyar da suka yi mata makarkashiya a lokacin zaben da ya gabata.

Ya yi nuni da cewa, shugabancin jam’iyyar ya kafa kwamitin da duba abin da ya faru da kuma dalilan faduwar jam’iyyar a zabukan 2023.

Ya kara da cewa PDP za ta dauki matakan da suka dace idan aka gabatar da rahoton ga kwamitin gudanarwa na kasa (NWC).

Damagum ya kuma nace cewa babu wanda ke sama da jam’iyyar, “idan Wike yana tunanin cewa yana sama da wannan jam’iyyar, za mu iya nuna masa iya gudun ruwansa.”

Ya ce: “A ko yaushe ina fadar cewar muddin kai dan jam’iyyar PDP ne, dole ne ka yi mata biyayya.

“Aikina shi ne na daidaita wannan jam’iyya ba haifar da rikici ba.

“Kuma zan ci gaba da yin hakan  sannu a hankali.

“Kuma, ba Wike kadai ba ne, akwai wasu mutanen da suka yi adawa da wannan jam’iyyar; idan muka kammala bincike za mu hukunta kowa.

“A halin yanzu, mun kafa kwamitin da zai yi bitar abubuwan da suka faru a 2023.

“Za su kawo mana rahoton abin da ya faru kuma duk wanda muka samu da laifi tabbas zai fuskanci hukunci,” in ji shi.

A makon jiya sakataren yada labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba ya ce shugabannin jam’iyyar na son mayar da hankali kan yin sulhu a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar da aka bata wa rai a baya maimakon saka kafar wando daya da su.