✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PDP ta lashe zaben Kananan Hukumomin Sakkwato

Jam’iyyar PDP ta lashe daukacin kujeru 247 da aka yi takara a zaben

Jam’iyyar PDP ta lashe daukacin kujerun 267 da aka yi takara a zaben Kananan Hukumoin Jihar Sakkwato.

Da yake sanar da sakamakon zaben, Shugaban Hukumar Zabe ta Jihar Sakkwato, Aliyu Suleiman, ya ce PDP ta lashe kujerun Shugabannin Kananan Hukumomi 23 da na Kansiloli 244 da ke Jihar.

“Na shaida cewa an gudanar da zaben cikin lumana kuma jami’iyyu 10 ne suka yi takara a cikinsa.

“’Yan takarar da suka yi nasara su ne suka samu kuri’u mafiya yawa sannan sun cika sharudan da doka ta shimfida.

“Saboda haka aka ina sanar da cewar su ne suka ci zaba kuma halastattun wadanda aka zaba,” inji shi a ranar Lahadi.

Sauran jam’iyyu da suka shiga zaben sun hada da Accord (AP), African Alliance (AA), African Democratic Congress (ADC), All Peoples Party (APP), African Progressive Movement (APM), Boot Party (BP), Peoples Democratic Party (PDP), Young Peoples Party (YPP), Zenith Party (ZP) da kuma Labour Party (LP).

Tun da farko dai babbar jam’iyyar adawa a Jihar, APC, ta sanar da kaurace wa zaben bisa zargin rufa-rufa.