✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta lashe zaben cike gurbi na mazabar Jos ta Arewa da Bassa

PDP ta yi nazarar a zaben ciki gurbi na dan Majalisar da ke wakiltar Jos ta Arewa da Bassa a Tarayya.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta bayyana Mista Musa Agah na jam’iyyar PDP, a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na dan Majalisar Wakilai ta Tarayya na mazabar Jos ta Arewa da Bassa da ke Jihar Filato.

Zaben cike gurbin wanda aka gudanar ranar Asabar ya biyo bayan rasuwar tsohon dan majalisar da ke wakiltar mazabar Jos ta Arewa da Bassa, Alhaji Haruna Maitala.

Da yake bayyana sakamakon zaben a safiyar ranar lahadi, babban jami’in Hukumar Zabe ta INEC da ya jagoranci zaben, Dokta Oyeyinka Oyeyinde, ya bayyana cewa Mista Musa Agah na jam’iyyar PDP, ya sami kuru’u 40,343 a zaben da aka gudanar.

Baturen zaben ya ce Gwani Adam Alkali na jam’iyyar PRP ya sami kuru’u 37,757 yayin da kuma Mista Joseph Abbey na jam’iyyar APC ya sami kuru’u 26,111 a zaben.

Oyeyinde ya ce don haka Mista Musa Agah na jam’iyyar PDP ne ya lashe wannan zabe.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Juma’a 2 ga watan Afrilun bara dan majalisar da ke wakilar mazabar Jos ta Arewa da Bassa, Alhaji Haruna Maitala, ya riga mu gidan gaskiya a wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Abuja zuwa Jos.