✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta kori wadanda suka dakatar da Ayu a Binuwai 

Matakin na zuwa ne bayan sa shugabannin mazabar suka dakatar da Ayu daga jam'iyyar PDP.

Kwamitin zartaswa na jam’iyyar PDP a Jihar Binuwai ya dakatar da shugabannin mazabar Igyorov da ke Karamar Hukumar Gboko a jihar.

Shugabannin mazabar ne suka dakatar da dakataccen shugaban jam’iyyar na kasa, Dokta Iyorchia Ayu.

A wani taron manema labarai a Makurdi, babban birnin Jihar Binuwai a ranar Alhamis, mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Isaac Mffo, ya ce dakatarwar za ta dauki tsawon wata guda.

Mffo, ya ce a lokacin dakatarwar, kwamitin zartarwar jam’iyyar na jihar zai dauki nauyin kula da harkokin jam’iyyar na mazabar Igyorov.

“An dakatar da kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP a gundumar Igyorov na tsawon wata guda har zuwa lokacin da al’amura za su daidaita jam’iyyar a yankin.

“Kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP a gundumar Igyorov za ta mika duk wasu takardu da sauran abubuwan da ke hannunsu na jam’iyyar ga kwamitin zartarwa na jam’iyyar na jiha ba tare da bata lokaci ba.

“Kwamitin ayyuka na jihar zai gudanar da al’amuran jam’iyyar a gundumar Igyorov har zuwa lokacin zartar da hukunci,” in ji shugaban jam’iyyar PDP na jihar.