Babbar Jam’iyyar adawa PDP ta yi sauye-sauye kan al’amuran da suka shafi babban zaben 2023 da ke kara karatowa.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na kasa, Mista Debo Ologunagba, ya fitar a daren Juma’a.
- Buhari ya yafe wa ‘kowane’ barawo kawai —Falana
- Masallacin da aka shekara 60 ba a fuskantar alkibla daidai
Ologunagba ya ce jam’iyyar ta kara wa’adin lokacin da za ta rufe sayar da fom ga ’yan takararta zuwa ranar Talata, 19 ga watan Afrilun 2022, yayin da kuma ranar Laraba, 20 ga watan Afrilu za ta kasance ranar mayar da fom din ’yan takara ga ofishin jam’iyyar.
Ologunagba ya ce jam’iyyar ta yi sauye-sauyen ne duba da samun ranakun Easter da suka fado cikin wa’adin da aka debar wa lokacin sayen fom takara.
Kazalika, ya ce jam’iyyar ta tsayar da ranar Juma’a 16 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za a fara tantance ‘yan takarar da suka sayi fom din ‘yan majalisar jiha.
A cewarsa, ranar Laraba 27 ga watan Afrilu, ita ce ranar da za a tantance ’yan takarar majalisar tarayya, yayin da ranar 29 ga watan Afrilu za ta zama ranar tantance masu neman takarar kujerar Gwamna, sai masu neman Shugaban Kasa ranar 30 ga watan na Afrilu.
Daga nan Sakataren ya ja hankalin wadanda suka yi sayi fom din kujerar ’yan majalisa da su yi kokarin cikewa tare sa mayar da shi ga sakatariyar jam’iyyar a kan lokaci.