A wani mataki na sasanta rikicin da ke ruruwa a PDP, kwamitin zartaswa na jam’iyyar a ranar Alhamis ya janye dakatarwar da ya yi wa wasu ’ya’yan jam’iyyar.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba ne, ya bayyana sunayen wadanda aka janye dakatarwar da suka hada da tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema da Ayodele Fayose daga Jihar Ekiti.
Sauran sun hada da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Anyim Pius Anyim daga Jihar Ebonyi, Farfesa Dennis Ityavyar daga Jihar Binuwai da kuma Dokta Aslam Aliyu daga Jihar Zamfara.
Kwamitin ya kuma janye mika Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom ga kwamitin ladabtarwarsa.
Matakin ya biyo bayan tattaunawa mai zurfi game da abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar a baya-bayan nan.
Kwamitin, wanda ke karkashin jagorancin Shugaban jam’iyyar na rikon kwarya, Umar Damagum ya ce sulhu a tsakanin shugabannin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki don samar da jam’iyya mai hadin kai baki daya shi ne dalilin da ya sa aka janye hukunci da aka dauka a kan su.
“Kwamitin ya bukaci dukkan shugabanni, masu ruwa da tsaki da jiga-jigan jam’iyyarmu a fadin kasar nan da su yi amfani da kundin tsarin mulkin PDP (wanda aka yi kwaskwarima a shekarar 2017) wajen yin sulhu da samar da hadin kai da zaman lafiya a tsakaninmu.
“Dole ne jam’iyyar PDP ta mayar da hankali yayin da muke ci gaba da daukar matakan da suka dace don kwato hakkinmu da ’yan Najeriya suka bai wa jam’iyyarmu da kuma dan takararmu na Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, 2023, a kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa.”
Tun da fari PDP ta dakatar da Anyim, Fayose da Shema kan zargin yi mata zagon kasa a zabukan da aka kammala na 2023.