Jam’iyyar PDP ta fitar da kwamitin da zai tantance wanda zai tsaya mata takarar Mataimakin Shugaban Kasa a babban zaben 2023.
Duk da jam’iyyar ba ta sanar da wanda ta fitar ba a hukumance, ana rade-radin Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike za ta ba wa tikitin takarar.
- Bankin Duniya zai ba Afirka ta Kudu rancen $474m don sayo rigakafin COVID-19
- Babu me yi wa Buhari katsa-landan a mulkinsa — Fadar Shugaban Kasa
Sai dai wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran jam’iyyar, Ologunagba ya fitar ya ce kwamitin na tafiya ne bisa sashe na hudu da na 14 na Kundin Dokokin jam’iyyar.
Ya kuma ce kwamitin zaben ya amince da fitsr da wasu ‘yan jam’iyar domin zamowa kwamitin tantance kujerar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.
Ya ce za a gudanar da tantancewar ce a hedkwatar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja ranar Alhamis, 16 ga watan Yunin 2022.
Chif Tom Ikimi dai shi ne jagoran kwamitin, sai sauran mambobin da suka hada da Kaftin Idris Wada mai ritaya, da Chif Osita Chidoka, da Honarabul Binta Bello, sai Honarabul Austin Opara da Farfesa Aisha Madawaki da Fidelis Tapgun.