✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta dage kamfe a Imo saboda harin da aka kai wa dan takararta

Jam'iyyar za ta gudanar da zanga-zangar nuna adawa da harin da aka kai wa dan takarar nata.

Jam’iyyar PDP a Jihar Imo, ta ce za ta dakatar da yakin neman zabenta bayan harin da aka kai gidan Ikenga Ugochinyere, dan takarar Majalisar Wakilai na jam’iyyar a mazabar Ideato ta Arewa da ta Kudu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren jam’iyyar na Jihar, Ray Emean, ya fitar ranar Talata.

Ya ce, za a dakatar da yakin neman zaben na tsawon mako guda, inda ya kara da cewa jam’iyyar ta kuma yanke shawarar gudanar da zanga-zanga kan harin da aka kai a mahaifar dan takarar a Akokwa, Imo.

Ya yi zargin cewa a ranar 14 ga watan Janairu, wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki gidan Ugochinyere, inda suka kashe mutum hudu ciki har da kawunsa.

Ugochinyere shi ne kakakin Gamayyar Jam’iyyu ta CUPP.

Emeana, ya ce za su shafe tsawon mako guda na zaman makoki, yayin da ya umarci duk masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da su dakatar da komai har bayan mako guda.

Ya ce za a yi zanga-zangar adawa da kisan ne a ranar 18 ga watan Janairu da misalin karfe 10 na safe.

Jihar Imo na daya daga cikin jihohin Kudancin Najeriya da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.

Ana dai zargin kungiyar ‘yan awaren Biyafara da kai hare-haren a wani yunkuri na hana gudanar da zabe da ke tafe.