✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PDP na taro kan yankin da zai fitar da dan takarar shugaban kasa

Kwamitin na son fitar da yankin da dan takarar shugaban kasa zai fito.

Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar PDP ya shiga wani muhimmin taro kan yankin da ya kamata ya fitar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023.

Wakilinmu ya ruwaito cewa taron yana gudana ne a masaukin gwamnan Jihar Benuwe a Abuja, wanda Samuel Ortom ke jagoranta.

Taron na da matukar muhimmanci domin ana sa ran kwamitin mai wakilai 37 zai fitar da sakamakon zaman nasa ga manema labarai.

Sai dai wasu na ganin kwamitin zai bai wa kowane yanki damar samun tikitin tsayar da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, sabanin yadda aka saba yi a baya.

Taron wanda aka fara shi da misalin karfe 12 na rana yana ci gaba da gudana har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Kwamitin jamiyyar bayan taron da ya yi na karshe, ya ba da shawarar kafa kwamitin shiyya mai mambobi 37 don yin watsi da wannan batu da ke barazana ga kawo cikas ga ’ya’yan jam’iyyar.

Hakan na zuwa ne bayan da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NEC), suka kasa cimma matsaya kan hanyar da za a bi.

Shugaban jam’iyyar na kasa dokta Iyorchia Ayu ne ya kaddamar da kwamitin tare da assasa tubalin hadin kan jam’iyyar a yunkurin lashe zaben shugaban kasa na 2023 da ke tafe.