✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PDP ce ta haifar da wahalar man fetur a Najeriya – Tinubu

Ya yi zargin mutanen da PDP ta ba lasisin dillancin man lokacin mulkinta ne yanzu ke zagon kasa

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya ce dillalan man da PDP ta bai wa lasisi zamanin mulkinta ne ke boye fetur yanzu a Najeriya.

Tinubu ya kuma ce magoya bayan PDPn da jam’iyyar ta bai wa lasisin zamanin mulkinta ne ke yin hakan saboda dalilan siyasa da kuma haddasa dogayen layuka a gidajen mai.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin gangamin yakin neman zabensa da ya gudanar a Jihar Binuwai ranar Alhamis.

Ya ce, PDP Jam’iyya ce ta ruruta wutar talauci ce, musamman idan aka yi la’akari da yadda ’yan Najeriya ke shan bakar wahala a yanzu.

“Sun bai wa magoya bayansu lasisin da yanzu ya haifar da dogayen layuka na jabu a gidajen mai. PDP haka ya ishe ku fa!”

Ya kuma ce rashin sanin doka ne ya sanya abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar, ya ce kasuwancin sufuri yake a lokacin da yake aiki da Hukumar Hana Fasakwauri ta Kasa, lokacin da yake amsa tambayar da wasu suka yi masa kan yadda ya yi arziki haka.

“Suka tambaye shi ya aka yi ya yi arzikin da yake da shi, sai ya kada baki ya ce kasuwancin sufuri yake. Bai san cewa laifi ne babba ba a ce kana ma’aikacin gwamnati kuma ka yi wani aikin ba noma ba,” in ji Tinubu.

Tsohon Gwamnan Jihar Legas din ya kuma ce yana da yakinin yadda ya ciyar da jiharsa gaba lokacin da ya jagoranceta, zai tabbatar ya yi wa Najeriya haka.