Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatocin da suka shude karkashin jam’iyyar PDP sun yi watsi da harkokin nakasassu a kasar nan baki daya. Shugaban ya bayyana haka ne a jawabinsa, jim kadan kafin ya kaddamar da wani katafariyar makarantar nakasassu ta zamani da gwamnatin Jihar Nasarawa ta kashe makudan kudi wajen gina ta a Lafiya fadar jihar.
Shugaba Buhari wanda ya ziyarci jihar don kaddamar da makarantar da kuma wasu ayyukan raya kasa da gwamnatin Umaru Tanko Al-makura ta yi, ya ce abin bakin ciki ne da takaici ayi watsi da harkokin nakasassu a kasar nan kasancewar Allah ne Ya haliccesu kamar yadda ya halicci kowa kuma suna da hakki a kasar nan.
Sakamakon haka acewarsa, rayuwar nakasassu a kasar nan ta zama abin tausayi, inda galibinsu suke barace-barace don su rayu, wadda hakan zubar da mutunci da darajarsu da na kasa ce baki daya a idon duniya. Sanna sai ya yabawa Gwamna Umaru Tanko Al-makura dangane da hangan nesa da ya yi na gina wannan makaranta inda ya ce ba shakka makarantar za ta je nesa ba kusa ba wajen sake fasalin rayuwar nakasassu a jihar da ma kasa baki daya.
Ya ce bai yi mamaki ba da ayyukan cigaba dake canja fasalin jihar da rayuwar al’ummarta baki daya da y azo ya gani ya kuma kaddamar a jihar ba, idan aka yi la’akari da akidojin jam’iyyar APC da acewarsa gwamna Almakura ke aiwatar wa tun da ya hau ragamar mulki a matsayin gwamnan jihar. Shugaba Buhari ya kuma bayyana cewa ba shakka jihar Nasarawa ita ce gidansa na siyasa domin jihar ce wace take gaba a wajen nuna masa cikakken goyon baya a tarihin siyasarsa kasancewar ita ce ta fito da gwamna daya tilo a fadin kasar nan a karkashin inuwar jam’iyyarsa ta CPC a 2011.
Ya ce gwamnatinsa za ta kuma hada hannu da gwamnatin jihar wajen kammala aikin gina babbar hanyar da ta taso daga garin Lafia zuwa Abuja don rage junkoso a hanyar Keffi da aka sabi bi zuwa Lafia. Game da rigirgimu da suka ki ci suka ki cinyewa tsakanin fulani makiyaya da manoma a garuruwa da kauyuka dake iyakokin jihar ta Nasarawa da Benuwai da sauran jihohin kasar nan, shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta cigaba da zura ido tana kallon wadannan miyagun mutane da ya bayyana cewa wasu fulani makiyaya da ‘yan fashi ke cin karensu babu babbaka wajen kisan al’ummar kasar nan ba gaira ba dalili, inda ya bayyana cewa bayan jami’an tsaro da a yanzu gwamnatin tarayya ta turo wadannan wurare za ta kuma karo wasu don kawo karshen rigirgimun baki daya. Daganan sai ya godewa gwamnati da al’ummar jihar baki daya da suka fiko kwansu da kwarkwata suka tarbe shi da tawagarsa cikin farin ciki da annashuwa.
Ana sa bangaren da yake jawabi, Gwamnan Jihar ta Nasarawa, Umaru Tanko Al-makura ya godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da amsa gayyatar da ya yi ba tare da bata lokaci ba zuwa jihar don kaddamar da wadannan ayyukan cigaba da gwamnatinsa ke yi ga al’ummar jihar, inda ya ce ba shakka babbar dama ce jihar ta samu na karbar bakuncin shugaban kasa. Ya ce soyayyar jihar dake zuciyar shugaba Buhari ne ya sa bai yi wata-wata ba ya amsa gayyatar.
A cewarsa ya na koyi ne da ayyukan cigaba a dukkan matakai da shugaban kasa ke yi ga al’ummar Najeriya baki daya ba tare da nuna bambancin addini, kabila ko siyasa ba. Shi yasa a cewarsa tun da ya hau mulki a matsayin gwamnan jihar bai yi wata-wata ba ya fara aiwatar da ayyukan raya kasa dake canja rayuwar al’ummar jihar.
A nasa jawabin, Ministan Ilmi, Malam Adamu Adamu ya bayyana gina makarantar nakasassu da Gwamna Al-makura ya yi da cewa mafarkin gwamnatin jihar da ma ta tarayya ce ya zama gaskiya. Ya ce wannan dama ce da ta zo wa duk wanda ke da nakasa ya samu ilmin addini da na zamani da sauran al’umma don dogara da kai. Ya jinjinawa gwamnatin jihar dangane da wannan namijin kokari da ta yi inda ya bayyana cewa a nata bangare, gwamnatin tarayya ta ma’aikatar ilimi na kasa za ta cigaba da tallafa wa kokarin gwamnatin jihar a wannan bangaren.
Sauran ayyukan da shugaban kasan ya kadddamar a yayin ziyarar na yini daya, sun hada da babban hedikwatar hukumar kashe gobara na jihar dake Lafia da dakin karatu na zamani dake Lafia da babban asibitin gwamnati dake Kwandere, da kuma duba babban filin saukar jiragein sama na zamani da gwamnatin Al-makura ke gina wa a Kwandere da babban kasuwar kasa da kasa na zamani dake Maraba a karamar Hukumar Karu wanda aka sanya wa suna; “Muhammadu Buhari International Market”. Ziyarar ta kuma samu halartar gwamnonin jihohin Benuwai da Filato dake makwabtaka da jihar ta Nasarawa.