✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PCNI ya tura jami’an kiwon lafiya zuwa Arewa maso Gabas

Kwamitin Shugaban kasa Kan Farfado da Arewa maso Gabas (PCNI), ya tura wani ayarin jami’an kiwon lafiya zuwa Arewa maso Gabas domin kula da bukatun…

Kwamitin Shugaban kasa Kan Farfado da Arewa maso Gabas (PCNI), ya tura wani ayarin jami’an kiwon lafiya zuwa Arewa maso Gabas domin kula da bukatun ’yan gudun hijira da suke zaune a sansanoni daban-daban a fannin kiwon lafiya. Shugaban Kwamitin Kula da Bayar da Taimako da Sake Tsugunnar da ’Yan Gudun Hijira na Kwamitin PCNI, Dokta Sidi-Ali Mohammed ne ya bayyana haka a zauren taron wata-wata da aka gudanar a ranar 25 ga Janairun bana a Abuja. Kwamitin jami’an kiwon lafiyar sun kammala ayyukansu a Yobe da Borno, inda nan ba da dadewa ba za su tafi Adamawa. Da zarar sun kammala da Adamawa kuma za su sake maimaita ziyarar tasu daga inda suka fara.

A cewar Dokta Mohammed, Kwamitin PCNI ya samu damar magance wasu muhimman bukatu na ’yan gudun hijirar kuma yana kan kula da dubban mutanen da aka raba da muhallinsu a karkashin shirin kula da lafiya cikin gaggawa. An tsara shirin ne domin ya taimaka wajen gudanar da sauran ayyukan kiwon lafiya na abokan hadin gwiwa tare da cike gibin da ake da shi kan kula da lafiya a yankin. Ya ce PCNI ya samu nasarori a fannoni da dama wajen biyan bukatun da suka zama lalura ga ’yan gudun hijira a jihohin da lamarin ya shafa, da suka hada da lafiya da ilmi da muhalli da kuma sake fasalin rarraba kayayyakin jin kai a sansanoni da kuma kauyuka.