Mataimakin Shugaban Kwamitin Shugaban kasa kan Arewa maso Gabas (PCNI), Alhaji Tijjani Tumsah, ya ce kwamitin da Asusun Tallafa wa Wadanda suka Jikkata (bSF), sun kashe sama da Naira biliyan shida a ayyukan tallafawa daban-daban a Arewa maso Gabas.
Alhaji Tijjani Tumsah ya bayyana haka ne lokacin kaddamar da sake ginawa da gyara wasu gine-ginen gwamnati da Asusun bSF ya gudanar a garin Michika a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ce an kashe fiye da Naira biliyan daya a Adamawa kadai. Za a sake ginawa da gyara gine-gine 13 a karamar Hukumar Michika da suka hada da Sakatariyar karamar Hukumar wadda za ta ci Naira miliyan 390. kananan hukumomin bakwai sun hada da Madagali da Michika da Maiha da Mubi ta Arewa da Mubi ta Kudu da Hong da Gombi, wadanda rikicin Boko Haram da hare-haren ta’addanci suka yi wa matukar shafa a Jihar Adamawa.
Alhaji Tumsah, ya ce adadin kudin da aka ware wa Jihar Adamawa an kashe su ne wajen tallafa wa gine-ginen gwamnati da kuma tallafa wa asibitoci 20 na yankin, don gudanar da ayyukan kula da lafiya kyauta ga wadanda tu’annatin Boko Haram ya jikkata. Ya yi bayani kan yadda aka samu nasarar dawowa da ’yan gudun hijira da sake tsugunar da su da kuma samar musu da kayan gini da tallafa wa harkokin rayuwarsu da na kasuwanci da kuma shirin farfado da makarantu da wadatattun kayan koyon karatu ga yara a matsayin sassan bayar da tallafi na musamman. Ya ce mata ne suka fi cin gajiyar shirin tallafin bunkasa rayuwa.
Alhaji Tumsah ya ce an kaddamar da irin wannan shirin tallfi a kananan hukumomin Bama da Dikwa a Jihar Barno da Buni-Yadi a Jihar Yobe. Sai ya yi kira ga wadanda suka ci gajiyar shirin su ci gaba da bayar da goyon baya ga Gwamnatin Tarayya wajen gyara da sake gina yankin Arewa maso Gabas.