Ministan Sadarwa, Malam Isa Ali Pantami ya je ta’aziya Kano gidan su Hanifa Abubakar, yarinya ’yar shekara biyar da ake tuhumar wani malamin makarantarsu da laifin kisan ta.
Kamar yadda ya wassafa a shafukansa na dandalan sada zumunta, Pantami ya yi ta’aziyya ga mahaifin yarinyar, Malam Abubakar.
- Harin IS ya raba mutum dubu 45 da muhallansu a Syria
- ’Yan bindiga sun kashe mutum daya, sun sace 15 a Neja
- Yadda mutumin da ake tuhuma da kashe Hanifa ya gurfana a Kotu
Haka kuma mahaifin Hanifa ya jagoranci shiga har cikin gida, inda Sheikh Pantami ya jajanta wa mahaifiya da sauran ’yan uwanta kan wannan babban rashi da suka yi.
Baya ga nasihohi, Ministan ya kuma tunatar da iyayen Hanifa muhimmanci da kuma wajibcin yin hakuri a lokacin jarrabawa mai tsanani makamanciyar wannan.
Cikin sakon da ya biyo hotunan ziyarar da ya wallafa, Ministan ya roki Allah Ya sanya marigayiya Hanifa Abubakar ta zama mai ceto a lahira ga iyayenta.
Ya kuma ba wa iyayen hakuri a kan wannan babban rashi da ya faru sanadiyar was azzalumai da suka nuna rashin imani.
A nasu bangaren, iyayen Hanifa sun yi godiya ga Malam da addu’ar fatan alheri a kan nasihohi da addu’o’i da ya gabatar.