✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Pakistan da Rasha za su sayar wa Najeriya jiragen yaqi

Babban Hafsan Sojin Sama Iya Mashal Sadikue Abubakar ya ce Najeriya tana jirar isowar jiragen yaki da helikwaftocin da ta yi oda daga kasashen Pakistan…

Babban Hafsan Sojin Sama Iya Mashal Sadikue Abubakar ya ce Najeriya tana jirar isowar jiragen yaki da helikwaftocin da ta yi oda daga kasashen Pakistan da Rasha a kokarinta na baya-bayan nan na kawar da ’yan ta’addan Boko Haram da ayyukan ’yan ta’addan yankin Neja-Delta.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ingila (Reuters) da ya ruwaito labarin ya ce Mashal Sadikue ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a Abuja.
Najeriya tana fama da mayakan Boko Haram a tsawon shekara bakwai da suka gabata a yankin Arewa maso Gabas a kokarin kungiyar na kafa daular Musulunci, kuma hare-harensu ya hallaka dubban mutane tare da tilasta fiye da miliyan biyu yin gudun hijira daga garuruwansu.
Sannan tana fuskantar barazana daga ’yan ta’addan yankin Neja-Delta mai albarkatun man fetur, inda suke sanya bama-bamai a bututun mai lamarin da ya jawo wa gwamnati asarar dimbin kudin shiga sakamakon koma baya wajen hako man a yankin.
Shugaban Sojin Saman ya ce jiragen yakin za a yi amfani da su ne wajen tallafa wa sojin sama da na ruwa kan yaki da ayyukan ’yan ta’adda da tsagerun Neja-Delta.
A wata Mayun da ya gabata, Ministan Harkokin kasashen Wajen Najeriya…………. ya ce gwamnatin tana fata kasar Amurka ta sayar wa kasar nan da jiragen yaki don yakar Boko Haram, saboda ta kara inganta kare hakkin dan Adam da za a iya janye mata takunkumin sayar da makamai.
Amurka ta sanya takunkumin sayar da makamai ga Najeriya ko ba ta tallafin horon soji a lokacin gwamnatin da ta gabata, saboda zargin tauye hakkin dan Adam musamman ga wadanda aka kama bisa zargin ’yan ta’adda ne.
Iya Mashal Abubakar bai yi bayani kan batun sayo makamani ba, amma ya ce rundunarsa tana samun tallafin da ya wajaba daga kasashe da dama musamman a fannin horar da sojoji.
Ya ce, fiye da sojin sama 700 suke samun horo a kasashen Pakistan da China da Ingila da Afirka tas Kudu da Masar da Rasha da kuma Amurka.
A wani labarin kuma Hafsan Hafsoshin Sojin kasa, Lafta Janar Tukur Buratai ya fadi a wata sanarwa cewa wajibi ne a rika tafiyar da harkokin ’yan ta’addana da aka kama kamar yadda dokokin duniya suka tsara, inda ya ce yana son ganin sojoji sun koma barikokinsu a badi.
Janar Buratai ya bukaci dukkan kwamandojinsa kan su rika aiki tare da sojin sama da na ruwa domin ceto wadanda ’yan Boko Haram suka sace su.