✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Pakistan: An haramta wa Imran Khan tsayawa takara

Hukumar Zabe ta Pakistan ta haramta wa tsohon fira ministan kasar Imran Khan tsayawa takara na shekara biyar kan zargin rashawa

Tarzoma ta barke bayan Hukumar Zabe ta Pakistan (ECP) ta haramta wa tsohon fira ministan kasar, Imran Khan, tsayawa takara na shekara biyar kan zargin rashawa.

Hukumar ta haramta masa takara ne bisa samun sa da laifin yi wa gwamnati karya game da kyaututtukan da shugabannin kasashen waje suka yi mishi a zamanin mulkinsa.

Sabuwar dambarwar siyasar ta kunno kai ne bayan wasu shari’o’i da tsohon shugaban da aka sauke a watan Afrilu tare da jam’iyyarsa ta PTI suke fuskanta.

Tarzoma a sasssan Pakistan

Tun bayan sanar da matakin a ranar Juma’a magoya bayan Imran Khan da PTI suka yi ta farfasa motoci bayan sun bar hedikwatar hukumar; ’yan sanda sun tsare wani mai gadin jam’iyyar bayan ya yi harbi a kasa.

Tuni dai aka yi ta zanga-zanga a sassan Pakistan, lamarin da ya sanya ’yan sanda harba hayaki mai sanya hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar da suka tare hanyoyi a Islamad, babban birnin kasar.

A wani bidiyo a ranar Juma’a, Imran Khan, ya yi kira ga magoya bayansa su kwantar da hankalinsu, yana cewa zai jagornaci tattakin magoya bayansa a Islamad kafin karshen watan Oktoba da muke ciki.

Ya ce, “Ina rokon ku da ku dakatar da zanga-zangar saboda tana cutar da mutane, sannan ba na kaunar ganin kasarmu ta shiga cikin matsala.”

Imran Khan zai garzaya kotu

Ya bayyana cewa zai kalubalanci hukuncin hukumar a kotu, yana mai zargin ta da hada baki da miyagu a gwamnati.

“Na dauki wannan abin fiye da siyasa, ina ganin sa a matsayin Jihadi.

“Matukar ina raye, zan ci gaba da yakar miyagun da ke cikin gwamnati, ciki har da shugaban hukumar zabe.”

Shari’ar zabe kan dauki tsawon lokaci a kotunan Pakistan, wanda kungiyoyin kare hakki ke zargin amfani da su wajen tadiye ’yan adawa.

Sai dai kuma matakin da ECP ta dauka kan Imran Khan na da alaka ne da bukatar zababbun su bayyana duk kadarorinsu.

Mene ne laifin Imran Khan?

Dambarwar ta samo asali ne daga bincike hukumar “Toshakhana”, wadda kayan alfarma da aka yi wa shugabannin kasar kyautar su.

Wajibi ne jami’ai su bayyana duk kyaututtukan da aka yi musu, amma an ba su damar ajiye wasu da darajarsu ba ta kai kimar da aka kayyade ba.

Abubuwa masu tsada kuma wajibi ne a mika su ga Toshakhana, amma a wasu lokuta wadanda aka yi wa kyautar kan iya sayen su a rabin kudinsu na ainihi – wanda Khan ya daga daga kashi 20% a zamanin mulkinsa.

Jaridun Pakistan sun yi watanni suna daukar rahotannin dake zargin Khan da matarsa sun karbi kyaututtukan alfarma akasashen waje da kudinsu ya kai miliyoyin daloli – ciki har da agoguna da gwala-gwalai da jakunkunan hannu da turaruka – kuma ba su bayyana ba.

Imran Khan ya ce bai bayyana an yi wasu kyaututtukan ba ne saboda dalilan tsaro.

Amma a wata takardar shaida da ya gabatar ya bayyana ceaw ya sayi was kyayyaki na Dala miliyan 22, kuma ya sayar da da su a kan Dala miliyan 44.