A ranar Litinin da ta gabata ne dan kwallon U-17 bictor Osimhen ya tafi Jamus don rattaba wa kulob din Wolfsburg hannu.
Kulob da dama ne suka yi zawarcin dan kwallon a sassan Turai ciki har da na Arsenal da kuma Manchester City da ke Ingila jim kadan bayan an kammala gasar cin kofin matasa na duniya (U-17) a bara, amma dan kwallon ya gwammace ya sanya wa Wolfsburg hannu saboda yadda kulob din ya lasa masa romo a baki.
Kafar sadarawar wasanni ta Goal.com ta kalato cewa an ga Osimhen tare da mahaifinsa da kuma wadansu daga cikin ’yan uwansa mata a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas a ranar Litinin da ta gabata a kokarin tafiya tare da mahaifinsa zuwa Jamus don a kammala yarjejeniyar kwantaragin a can.
Ana sa ran kafin karshen wannan mako ne dan kwallon zai rattaba hannu a kwanataragin.
Osimhen ne ya kafa sabon tarihi a gasar cin kofin duniya na matasa na ’yan kasa da shekara 17 (U-17) bayan ya zura kwallaye 10 a raga a gasar da ta gudana a Chile a bara.
Tun daga wannan lokaci ne kulob da dama a Nahiyar Turai suka rika rububinsa.
Osimhen ya tafi Jamus don sanya wa kulob din Wolfsburg hannu
A ranar Litinin da ta gabata ne dan kwallon U-17 bictor Osimhen ya tafi Jamus don rattaba wa kulob din Wolfsburg hannu.Kulob da dama ne…