dan kwallon gaba a kungiyar Golden Eaglets da ya kafa tarihin wanda ya fi kowa zura kwallo a raga bictor Osimhen da kuma Kyaftin din kungiyar Kelechi Nwakali sun yaba wa kocinsu Emmanuel Amunike bisa damar da ya ba su har suka samu nasara a gasar cin kofin duniya na matasa na ’yan kasa da shekara 17 da aka kammala a Chile a ranar Lahadin da ta wuce.
Osimhen wanda ya zura kwallaye 10 a raga a yayin gasar ya yaba wa kocinsa Amunike ne ganin yadda ya zakulo shi kuma ya ba shi dama a gasar da ta sa yanzu haka ya yi fice a duniya. kwallo daya da kuma wacce Funsho Bambboye suka zura a ragar Mali ce ta ba kungiyar damar lashe kofin a wasan karshe a ranar Lahadin da ta wuce a gaban ’yan kallo fiye da dubu 21 ciki har da shugaban Hukumar NFF Mista Amaju Pinnick a filin wasa na Chile. Rahotanni sun nuna da yawa daga cikin ’yan Najeriya mazauna Ajantina sun yi tattaki zuwa Chile don mara wa Golden Eaglets baya a wasan karshen.
bictor Osimhen ne ya lashe kyautar takalmin zinare (Golden Boot) bayan ya zura kwallaye 10 a raga Ya sadaukar da kyautar da ya samu ne ga kanwarsa da ke aure a Najeriya wacce ya haifi ’ya mace a ranar Juma’ar da ta wuce watau ana saura kwana biyu Golden Eaglets ta buga wasan karshe da Mali.
Shi ma kyaftin din kungiyar Eaglets Kelechi Nwakali ya yaba wa koci Emmanuel Amunike ne bayan ya ba shi dama a gasar. Kelechi wanda bai samu halartar irin wannan gasa da ta gudana a shekarar 2013 a Dubai ba bayan an cire sunansa daga cikin tawagar ’yan kwallon ana gab da tafiya gasar a wancan lokaci, a wannan karo Amunike ya sake gayyatarsa ne don ya ba shi dama. Hakan ta sa ya samu dama a wannan karo a matsayinsa na kyaftin din kungiyar ya daga kofin duniya a karon farko a tarihin rayuwarsa. “Burin kowane dan kwallo ne ya daga kofin duniya, sai ga shi na cimma burina a wannan lokaci bayan Amunike ya ba ni dama, a gaskiya ina mika godiyata ta musamman a gare shi, don ya zama tamkar uba a gare mu baki daya”.
Nwakali ne aka zaba a matsayin dan kwallon da ya fi kokari a gasar (Most baluable Player) inda aka ba shi kyautar kwallon zinare (Golden Ball).
Tuni ’yan kwallon Golden Eaglets suka cigaba da samun yabo a ciki da wajen Najeriya saboda namijin kokarin da suka yi na lashe kofin duniya na ’yan kasa da shekara 17 sau biyu a jere kuma na biyar a tarihin gasar.