✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Oscar Pistorious zai shafe shekara 5 a gidan yari

Bayan an kwashe kusan shekara guda ana turka-turka a shari’ar da ake wa shahararren dan gudun nakasassu na Afirka ta Kudu Oscar Pistorious, a ranar…

Bayan an kwashe kusan shekara guda ana turka-turka a shari’ar da ake wa shahararren dan gudun nakasassu na Afirka ta Kudu Oscar Pistorious, a ranar Talatar da ta gabata ne wata kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekara biyar a gidan yari bayan an same shi da laifin kashe budurwarsa mai suna Reeba Steenkamp a shekarar 2013.

Shi dai Oscar ya harbe budurwarsa ce a shekarar 2013 a lokacin da ta ziyarce shi a gidansa da sassafe ba tare da saninsa ba al’amarin da ya sa ya harbeta da bindiga har sau hudu a zatonsa barawo ne yake kokarin shigar masa gida da hakan ya sa ta fadi nan take a mace.
Iyalan marigayiyar ne suka shigar da kara don a bi musu kadi a kan wannan danyen aiki da Oscar ya aikata musu. Sai dai Oscar Pistorious ya yi nadamar abin da ya aikata inda ya ce, ya yi haka ne bisa kuskure ba da gangan ba.
Bayan kotun ta saurari dukkan bangarorin biyu ne sai Babbar alkalin kotu mai suna Thokozile Masipa ta yanke masa hukuncin daurin shekara biyar a gidan yari.
Iyalan marigayiyar sun yi yunkurin an yanke wa Oscar hukuncin kisa ne don ya zama darasi a gare shi amma sai ya samu sassaucin kotu na daure shi shekara biyar.