Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ta amince da wani tsarin da zai iya kaiwa ga matakin karin farashin man fetur duk kuwa da hauhawar farashin danyen man da kuma kalubalen da ke taka rawa a kasuwannin duniya.
Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce kasashen da Saudiya da Rasha ke jagoranta za su kara yawan man da suke hakowa da ganga 400,000 a kowace rana a cikin watan Maris, tare da kiyaye manufofin da aka yi a watannin baya.
- Gwamnatin Tarayya ta gano masu daukar nauyin ta’addanci 96
- Fitinar Boko Haram somin tabi ce idan ISWAP ta bunkasa —Zulum
Masana tattalin arziki sunce tuni kungiyar ta OPEC mai mabobin kasashe 23 ke fafutukar ganin ta cimma kason da ta ke da shi da wasu kasashe kamar Angola da Najeriya da ba za su iya habaka hanyoyin hako da man ba da sauransu kamar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa ba.
A cikin watan Disamba, jimillar adadin albarkatun da OPEC ke fitarwa ya karu da ganga 90,000 a kowace rana, wanda haura 400,000 da ake son cimmawa, a cewar wani bincike na kamfanin dillancin labarai na Bloomberg.
Masana dai na ganin kasuwar ta kara samun habaka ne sakamakon tashe-tashen hankulan da suka addabi jiga-jigan kasashen da ke samar da mai, wato Rasha, Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa.
A ranar Litinin ce Hadaddiyar Daular Larabawa ta sake kakkabo wani makami mai linzami da ‘yan tawayen Huthi na Yaman suka harba, wanda shi ne hari na baya-bayan nan da aka kai wa kasar, wadda ke cikin kawancen sojan da Saudiyya ke jagoranta.
Gidan Rediyon Faransa RFI ya ruwaito cewa, a Turai, zaman dar-dar tsakanin Rasha da kawayenta na Yamma ya kai matsayin mafi girma tun bayan yakin cacar-baka bayan da fadar Kremlin ta tara sojoji a kan iyakarta da Ukraine.