Hukumar kula da Ma’aikatan Majalisar Tarayya (NASC) ta bai wa Mista Ojo Amos Olatunde, matsayin mukaddashin Magatakardan Majalisar Tarayya.
Hakan yana kunshe ne a wata takardar da shugaban hukumar, Ahmed Khadi Amshi, ya rattaba wa hannu a ranar Juma’a, bayan taron da suka yi na gaugawa.
Hukumar ta kuma nada: Bala Yabani Mohammed a matsayin Mataimakin Magatakarda da Dauda Ibrahim El-Ladan a matsayin Mukaddashin Magatakarda Bangaren Sanatoci da Yusuf Asir Danbatta a matsayin Mataimakin Sakataren Hukumar mai kula da Ma’aikatan Majalissar.
Patrick A. Giwa, Magatakardan Majalissar Wakilai mai ci, zai ci gaba da rike wajen kafin wa’adin shekarun aikinsa ya kare cikin watan Nuwamba, 2020.
Ya kuma kara da cewar kowanensu ya je ya ci gaba da gudanar da aikinsa ba tare da bata lokaci ba.
Nada Olatunde a matsayin magatakarda zai kawo karshen rikicin da aka kwashe watanni ana yi na hana tsohon magatakardan, Mohammed Sani-Omolori zarcewa.
Idan ba a manta ba, hukumar ta umurci Sani-Omolori da wasu ma’aikata 150 su tafi hutun yiin ritaya sakamakon cikar wa’adin ayyukansu da ya yi na shekaru 35.
Sai dai a wata takarda da Sani-Omolori ya fitar, ya kalubalanci matakin da hukumar ta zarta, inda ya ce ba ta hurumin sallamar su bayan dokar Majalissar ta amince musu zarcewa.
Ya ce doka ta tabbatar da kara wa’adin shekarun aiki ga ma’aikatan Majalisar daga 35 zuwa 40, sai kuma shekaru 60 zuwa 65 na haihuwa.
Hakan ya sa Hukumar Ma’aikatan ta tilasta Sani-Omolori ya amsa tambayoyi kan karan-tsaye da rashin biyayyar da ya yi mata.
Shugaban hukumar ya ce Sani-Omolori bai isa ya nuna musu yadda za su gudanar da ayyukan ma’aikatan Majalisar ba.