Kungiyar Kasashe Musulmi (OIC) ta bukaci kasashen duniya da su janye wasu takunkuman karya tattalin arzikin da suka kakaba wa wasu kasashen Musulmi.
OIC, a yayin taron da ta gudanar a kasar Pakistan, ta ce a halin da duniya ke ciki na fama da talauci a kusan kowace kasa, akwai bukatar manyan kasashen duniya su sake tunani game da takunkuman da suka lafta wa wasu daga cikin kasashen Musulmi, musamman Afghanistan.
Kazalika, kungiyar ta ce ko kasar Pakistan tana fuskantar takunkumi kan rikicin da aka shafe shekaru ana yi da Kashmir.
Ministan Harkokin Wajen China, Wang Yi, ya halarci taron saboda zargin da ake wa kasarsa da yi wa Musulmin yankin Uyhgur kisan kare dangi, tare da tsare ’yan kabilar sama da miliyan daya a sansanonin azabtarwa.
Kazalika, taron ya tattauna kan yadda za a kawar da alakanta addinin Musulunci da ta’addanci, da kuma batun masu tsattsauran ra’ayin addini da kuma masu batanci ga addinin.
Taron wanda ya samu halatartar kasashen Musulmi 57 ya kuma bukaci a samar da hukuncin bai-daya kan duk wanda aka kama da laifin batanci ga addinin.